‘Yan sanda sun cafke matashin da ya yi garkuwa da mahaifinsa a Kwara

Daga WAKILINMU

Ana zargin wani matashi da yin garkuwa da mahaifinsa a Jihar Kwara inda ya buƙaci a biya fansar miliyan N2.5.

A sanarwar manema labarai da ya fitar a Ilorin Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya ce jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane a jihar sun cafke yaron.

“Yayin bincike wanda ake zargin ya yi ikirarin yin garkuwa da mahaifin nasa bayan haɗa baki da wasu mutum biyu.

“Lamarin ya auku ne a yankin Igboho/Igbeti Oyo inda suka karɓi kuɗin fansa N2.5m ransom,” in ji shi.

Jami’in ya ce suna ci gaba da bincike don kamo sauran da ke da hannu a badaƙalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *