Sarkin Kano, Aminu Bayero ya angonce

Daga WAKILINMU

A ranar Juma’a aka ɗaura auren Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da amaryarsa Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko.

An ɗaura Auren ne a gidan marigayi Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nassarawa a birnin Kano.

Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Cigari, shi ne ya kasance wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya yi waliccin amarya.

Majiyarmu ta ce tun a shekarar da ta gabata aka yi baikon basaraken da amaryarsa inda sai a wannan lokaci aka ɗaura auren.

An ce amaryar zuri’ar marigayi Malam Jamo ne wanda ɗan uwa yake ga marigayi Sarkin Kano na biyu a daular Sarakunan Fulani Malam Ibrahim Dabo.

Daga cikin waɗanda duka halarci ɗauri auren sun haɗa da Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar tofa da Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano, Alhaji Bello Abubakar Tuta da Ɗan Ruwatan Ringim da saurnsu.