Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC), ta ce ayyukan masu damfarar intanet da aka fi sani da Yahoo na janyo wa tattalin arzikin Nijeriya asara mai girma fiye da kowace ƙungiya a halin yanzu.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya jaddada cewa yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa ba na gwamnati kaɗai ba ne, illa lamari ne da ke buƙatar haɗin kan kowa da kowa.
A cewarsa, “Gaskiyar da muke fuskanta a yau a ƙasar nan ita ce masu damfarar intanet, wato ’Yan Yahoo, na haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin Nijeriya fiye da kowace ƙungiya. Ayyukansu na ci gaba da raunana tsarin tattalin arziki da kuma toshe hanyoyin ci gaba.”
Oyewale ya ce, damfarar intanet ta wuce batun asarar kuɗi kaɗai, domin tana lalata sunan Nijeriya a idon duniya, tana hana zuba jari, tare da haddasa matsaloli ga matasa da ake jan hankalinsu zuwa harkokin laifi maimakon aikin yi na halal.
Sai dai wannan furuci na EFCC ya tayar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda ‘yan Nijeriya da dama ke tambaya kan dalilin da ya sa hukumar ke mayar da hankali kan masu damfarar intanet, alhali a cewarsu har yanzu ana fama da gagarumin cin hanci a matakan manyan gwamnati.
Wasu masu sharhi sun bayyana cewa babu shakka ‘Yan Yahoo na janyo illar tattalin arziki da ɓata sunan ƙasa, amma sun ce ya kamata yaƙi da cin hanci ya kasance daidaito, ta yadda za a hukunta masu laifi a kowane mataki, ciki har da manyan jami’an gwamnati.
Tun a shekarar 2002 ne aka kafa EFCC a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban aasa Olusegun Obasanjo ta hanyar dokar Majalisar ƙasa, yayin da hukumar ta fara cikakken aiki a watan Afrilun 2003. An ɗorawa EFCC alhakin yaƙi da cin hanci da rashawa, damfarar kuɗi da sauran laifukan tattalin arziki, ciki har da na intanet.
EFCC ta ce, za ta ci gaba da matsa ƙaimi wajen yaƙi da masu damfarar intanet tare da sauran masu aikata laifukan kuɗi, tana mai kira ga al’umma da su ba da haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da kuma guje wa duk wata hanya ta samun kuɗi ta haramtacciyar hanya.
