Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Kungiyar Maitaimako Organisation da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, tsohon ɗan majalisar jiha na ƙaramar hukumar, wanda kuma yanzu hadimi ne a ofishin ƙaramin Ministan Gidaje da raya birane , Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo da aka fi sani da Alhajin Bana ta ƙaddamar da tsohon ɗan takarar Gwamnan Kano, Malam Salihu Sagir Takai a matsayin daraktan yaƙin neman zaɓe na Sanata Barau Jibrin na Gwamnan Kano
ƙungiyar ta Maitaimako ta ƙaddamar da Malam Salihu Takai ne a yayin taron cika shekara 23 da kafa ta da aka gudanar a babban ɗakin taro na gidan Mambayya a yammacin ranar Lahadi.
ƙaramin Ministan Gidaje na Nijeriya, Hon. Yusuf Abdullahi Ata, wanda ya halarci taron a jawabinsa ya ce, tsawon shekaru 23 da kafa ƙungiyar ta Maitaimako da Alhajin Baba ya kafa suna tare da shi a Kabuga suke zama da shi suke tattaunawa al’amuran siyasa, ko zuwan Buhari na farko shi da Alhajin Baba da Hajiya Naja suka je Kalebawa hanyar ɗanbatta suka taro Buhari lokacin da ya soma zuwa Kano.
ƙaramin Ministan Gidajen ya ce yana cikin jin daɗi da alfahari da ya zama har yanzu alaƙar tana nan. Ya yi fatan Allah ya ƙara musu jagora, kuma ya yi godiya ga al’ummar ƙaramar hukumar Birnin Kano da na Gwale, Dala, Fagge, Tarauni, Nassarawa, Kumbotso da Ungogo saboda duk lokacin da suka zo Kano yawanci suna fita da Alhajin Baba su biyu su sauke gilashin mota suna zagawa idan mutune suka gan su sai su riƙa fitowa suna sai Nababa sai na babba wannan abin jin daɗi ne.
Shi ma Shugaban da ya kafa Maitaimako Organisation, Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo Hadimi ga ƙaramin Ministan Gidaje na Tarayya, ya bayyana cewa ƙungiyar ta haifar da alherai masu yawa. Ita ta bayar da gudunmawa fiye da kashi 50 acikin 100 na zaman Malam Ibrahim Shekarau Gwamnan jihar Kano, ta kuma ba da gudunmawa ba na wasa ba a matsayin Abba Kabir Yusuf ya zama Gwamnan jihar Kano domin ita ta fara ƙaddamar da taron Abba Kabir a unguwar Gudundi.
Ya ƙara da cewa ita ce kuma ta ƙaddamar da takarar Malam Salihu Sagir Takai a jihar Kano, yau kuma ga shi cikin ikon Allah ta ƙaddamar da Malam Salihu Sagir Takai a matsayin daraktan yaƙin zaɓen Barau Jibrin Maliya na neman takarar Gwamnan jihar Kano.
Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo ya ce a ƙaramar hukumar Birnin Kano da kewaye kuwa duk wanda ake tsammani ƙungiyar ta ba shi gudunmawa sai dai mutum ya ƙi Allah ya ƙi faɗa, amma duk wanda ya ɗaga hannu da wanda yake cara da wanda yake raye da wanda ya rasu ƙungiyar ta ba shi gudunmawa, kuma in Allah ya yarda sai ta cigaba da haifar da Gwamna a jihar Kano, kuma a cikinta wata rana ko suna raye ko ba sa raye sai an fitar da Gwamna daga cikinta.
Alhajin Baba ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da cewa su guji siyasa ta son zuciya. “Abin da ke faruwa a jihar Kano daga iyayensu na siyasa da Malam Ibrahim Shekarau da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun fi kowa morar dimakwaraɗiyya a Kano, amma sun ƙi yarda ta yi aiki hakan ba daidai ba ne domin ita dimakwaraɗiyya lokacin da mutane suke hidima ga al’umma, kuma a wani gefe a ce an naɗa wane ba tsari ba ne babu dimakwaraɗiyya a hakan,” inji shi.
Salisu Ahmad Maje Ahmad ya yi nuni da Shekarau da Kwankwaso da Ganduje duk da zaɓen fid da gwani ingantacce suka zama Gwamna babu wanda mai gidansa ya ɗauei shi ya saka shi dimakwaraɗiyya ce ta kawo su, don haka su ƙyalle ta ta yi aiki a jihar Kano.
Shi ma a nasa ɓangaren, Darakta Janar na ƙungiyar Maitaimako. Hon. Nasiru Sani Hanga ya ce, abin farin ciki ne da jin daɗi tafiyar da ƙungiyar take tsawon wannan lokaci ta tallafa wa cigaban yara da manya da maza da mata, tafiya ce da aka daɗe ana gwagwarmayar siyasa a cikinta.
Hanga ya ƙara da cewa in aka yi duba da yadda kowa ya halarci taron ya ga yadda wajen ya cika ya san cewa an yi wani abu da mutane suka yaba sukaji daɗi wanda shi ne ya kawo albarkar tafiyar ƙungiyar suna fata iya cigaba da ɗaukaka ƙungiyar da ikon yadda za a cigaba da taimakon al’umma.
A taron dai ya sami halartar tsofaffin muƙarraban gwamnatin APC na jihar Kano da ɗan Majalisar jiha na Tsanyawa da Ghari, Hon. Gwarmai da wakilin ɗan Majalisar Tarayyar na ƙaramar hukumar Birni Injiniya Sagir ƙoƙi da tsohon Kantoman riƙo na ƙaramar hukumar Birnin Kano, Hon. Bashir Chilla ya wakilta da shugaban ma’aikata na ofishin mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Farfesa Bn Abdallah da sauran mutane da dama.
A yayin taron ƙungiyar ta karrama mutum huɗu daga cikin akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Bara’u I Jibrin da Malam Salihu Sagir Takai da ƙaramin Ministan Gidaje Yusuf Ata.
ƙungiyar ta kuma raba kyautar babura guda 17 ga matasa daga mazaɓun ƙaramar hukumar Birnin Kano.
