‘Yan zanga-zanga sun ƙi amincewa da buƙatar Sufeton ‘Yan sanda ta yi a keɓaɓɓun wurare saɓanin kan titina

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Talata ne waɗanda su ka shirya zanga-zangar ‘EndBadGovernance’ da za a yi a watan Agusta su ka ƙi amincewa da buƙatar Sufeton ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun, ta neman su gudanar da ita a keɓaɓɓun wurare madadin fitowa kan tituna.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da tsare-tsaren yadda zanga-zangar za ta gudana, a wani zama da aka yi da jagororin tafiyar da rundunar ƴan sandan.

Egbetokun ya ce “ba dai-dai ba ne a yi gangami a kan titi da nufin yin zanga-zanga. Wasu kuma na shirya yin tashin-tashina”.

Lauya Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) da ke kare tawagar ‘Take it Back Movement’, ɗaya daga cikin waɗanda ke shirya zanga-zangar, ya ce ba su amince da buƙatar Sufeton ba.

A ranar 26 ga watan Yuli ne Adegboruwa ya rubuta takarda ga Sufeton wacce a ciki ya nemi da ya samar da tsaro na dakarun rundunar ‘Yan sanda ga masu zanga-zangar.

Rundunar ‘Yan sanda da na soji da kuma ƴan sandan farin kaya ta DSS sun gargaɗi al’umma kan irin yadda ta faru a ƙasar Kenya.

Duk da cewa ƴan siyasa sun yi ta rarrashin masu zanga-zangar tare da buga misali da yadda ya faru lokacin ‘EndSars’ a Oktoban 2020 wajen ganin an janye daga batun yin zanga-zangar, amma matasan sun tirje, su na masu haƙiƙancewa sai sun yi.

By Babaji