Wata babbar kotu a Legas ta bada umarnin yin zanga-zanga a Peace Park da Freedom Park kaɗai ba faɗin Jihar Legas ba. Mai shari’a Emmanuel Ogundare shi ya bayar da wannan hukunci.
In ba mu manta ba, ‘yan Nijeriya a faɗin ƙasar na shirin gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a ranar ɗaya ga watan Agusta 2024.
Wani babban Lauya Lawal Pedro shine ya shigar da ƙarar, yana mai faɗin cewa, ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga amma bai kamata su mamaye ko ina ba domin gudun shiga haƙƙin waɗanda ba za su shiga zanga-zangar ba.
Pedro ya cigaba da cewa, haka zalika, rundunar ƴan sanda ba ta da isassun jami’ai da zasu ba da kariya da masu zanga-zangar a wurare da dama. Dole a san wurin da za a gudanar domin bada isashen kariya ga masu zanga-zangar saboda kar ɓatagari su shiga su aikata laifuka da dama.
