Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana muhimmancin kula da walwala da jin daɗin jami’an tsaron ƙasar nan yadda ya kamata zai taimaka wajen sawa su jajirce wajen gudanar da ayyukansu na samar da tsaro ga al’umma.
Dan kasuwa, basarake, ɗan siyasa, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ne ya bayyana hakan cikin makon nan a Kano.
Ya ce jami’an tsaro musamman ‘yan sanda koyaushe sai kuka suke na rashin kyakkyawan kulawa wasu ma sun gama aikin sun yi ritaya amma ɗan haƙƙin da za a basu an karkatar da shi ta wani tsari da basa iya samu cikin dakin rai da hakan tasa suka fito har suke zanga-zanga.
Ya ce ba ɓangaren jami’an tsaro kaɗai ba hatta fannin shari’a akwai buƙatar a samar da gyara ta yadda za a kiyaye mutuncinta da kimarta a ƙasar anan domin da yawa ana yin hukunci mai sassauci ga masu laifi sai mutum ya yi kisa amma sai daga baya a sake shi wannan yana taimakawa wajen ƙara ingiza yin laifuka.
Ya ce muddin za a gyara ɓangaren shari’a ya tafi yadda ya dace bisa adalci a inganta harkar jami’an tsaron hakan zai taimaka wajen a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali dole ‘yan majalisu na tarayya dana jihohi da sanatoci su tsaya a tsaftace tsarin.
Ya ƙara jaddada cewa muhimmancin shari’a na adalci shine tsaftace komai domin idan babu ingantacciyar shari’a babu zaman lafiya da kwanciyar hankali dole a tsaya a kula da tsarin doka jami’an tsaro suyi aikinsu na hana laifi su kuma masu sharia su yi aiki bisa adalci kada a yi musu matsala don daga gwamnati.
Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya ce, abin takaici sai kaga ana sakaci da doka a ƙasarnan ana zuwa da son rai saboda kawai ra’ayi na bambancin siyasa domin irin abinda yake faruwa a Kano kowa yasan Gwamna shine babban mai kula da tsaro na jiha da doka ta ba shi dama amma saboda wasu an hana yan sanda su karbi umarni da ga Gwamna musamman akan harkar sarakuna wanda ya yi komai ne bisa tsarin doka, amma wasu daga sama na yin abinda ya saɓa wa doka domin cutar da Kano.
