Babbar nasarata ita ce samun kaina a fim ɗin da aka kashe sama da miliyan ɗari a yin sa
Daga IBRAHIM HAMISU
Fatima Mohammad tana ɗaya daga cikin matasan jarumai da suke haskawa yanzu a masana’artar fim ta Kannywood harma da Nollywood, a tattauntawar da Ibrahim Hamisu a Kano ya yi da ita, za ku ji tarihinta da kuma irin yadda a cikin shekara 2 ta yi finafinai fiye da 20. Kuma ta jarorancin fim ɗin da aka kashe fiye da Miliyan 100 wanda yanzu haka a Kannywood babu fim ɗin da aka kashe kuɗi kamarsa, wato fim ɗin ‘Mai Martaba’.
A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?
FATIMA: Sunana Fatima Mohammed, wacce aka fi sani da Sangaya.
Ba mu taƙaitaccen tarihinii?
An haife ni a garin Maiduguri na girma a Abuja. Na yi primary a Abuja, na yi Secondary a Nasarawa state, sai na koma Maiduguri dan yin jarrabawar Waec da Neco.
Ta yaya kika samu kanki a masana’artar Kannywood?
Ikon Allah kenan tunda ba abu ne wanda za kace ka daɗe kana son yi ba.
Me ya baki sha’awa kika shiga Kannywood alhali wasu na ganin ku yi aure kawai shi ya fi da ku shiga harkar fim?
Kasan bawa ba zai tsallake kaddararsa ba, kuma ai aure lokaci ne idan lokacin ya yi dole za mu yi koda muna fim ko ba ma yi ko mun shirya ko bamu shirya ba, sai munyi idan lokacin ya yi.
A wane ɓangare kika fi ƙwarewa?
Na ɗauki fim sana’a saboda haka duk role ɗin da aka ba ni zan yi iya ƙoƙarina donn naga na bada abin da ake so.
A wacce shekara kika shiga Kannywood?
A shekara ta 2022.
Da wane fim kika fara?
Da fim cin ‘Mai Martaba’.
Kinyi finafinai za su kai nawa?
Na yi finafinai da dama a cikin shekaru biyu, duk da cewa, ba na kirgawa amma aƙalla za su kai guda 20.
Waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu ya zuwa yanzu a Kannywood?
Alhamdulillah, nasara ta farko ita ce samun kaina da na yi a cikin aikin ‘Mai Martaba’ wanda masana’antar Nollywood ta tsallako cikin wannan masana’antar mu ta shirya. Fim ne wanda yake da budget ɗin da ya wuce Naira miliyan dari. Na ja ragamar wannan shiri wanda aka haska a cikin sinimomi da suke cikin ƙasar Nijeriya.
Har ila yau dai, shi wannan fim ɗin ya ba ni nasarar shiga cikin jerin gwanon mutum biyar na Amma Award suka zaɓa a matsayin Best Young Coming Up Actress wanda ina da yaƙinin ni ce zan zo na ɗaya a cikin mutane biyar ɗin.
Ƙalubale fa akawai ko babu ?
Ƙalubale na shi ne yin sammakon zuwa wajan aiki wani lokacin sai dare zaka koma gida, rashin samun lokacin kanka saboda aikin mutane da ka karɓa da sauran su.
Wane ne maigidanki a Kannywood?
Iyayen gidana ba wai iya Kannywood ba ne har da Nollywood, akwai Prince Daniel Aboki da kuma Kamilu Ibrahim Dan Hausa.
Kin taɓa samun shaidar karramawa a Kannywood?
A’a sai dai a wajan Kannywood wato (Nollywood) Wanda yanzu ina cikin biyar Nominee’s na Best young coming Actor/Actress da AMA Award suke tantancewa wanda Insha Allah ina sa ran ni ce zan zama zakaran gwajin dafin idan Allah ya yarda.
Me kike so ki zama a nan gaba a fagen masana’antar fim?
Ina so na zama mai bada umurni (Director) wacce duk duniya zata sanni da ayyuka na kuma ba iya kannywood ba har gaba da kannywood. Don yana daga cikin burina na lashe Oscar Award amatsayin Director
Da me kike so a tunaki?
Ingantattacen aikina da nasarorina.
Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

