Daga shekarar 1999 zuwa 2011, ɗan Nijeriya yana iya bugun ƙirjin cewa yana alfahari da ƙasarsa, domin ko babu komai a wancan lokacin akwai sauƙin rayuwa fiye da irin rayuwar da ake yi yanzu, musamman ga Malam talaka.
Haka nan duk da faruwar ayyukan ‘yan ƙungiyar masu da’awar jihadi ta Boko Haram, da suka fara ayyukansu gadan-gadan a shekarar, har zuwa shekarar 2015, talakawan Nijeriya babu wani abu na damuwa da yake damunsu sai ayyukan ‘yan boko haram ɗin, da ɗaiɗaikun ayyukan garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa, da kuma rikicin manoma da makiyaya.
An tara maƙudan kuɗi a Nijeriya a lokacin mulkin Marigayi Umar Musa ‘Yar’adua, kuma an ƙirƙiro manyan ayyukan raya ƙasa da bunƙasa al’umma, kamar gina kogin da zai kawo ruwa Arewa, da shirin gina babbar cibiyar lantarki a Arewa, samar da layin dogo (titin jirgin ƙasa) don ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci, rage farashin albarkatun mai irin su; fetur, gas da sauransu. Wanda tsohon shugaban ƙasa Marigayi ‘Yar’adua yasa aka riƙa karɓar hayar gidajen mai (musamman wanda suke ganin ba za su iya siyar da man fetur kan farashin Gwamnati na N65 a kan kowacce lita ba), tare da gina sabbi.
Ko shakka babu! Wannan mataki da Marigayi tsohon shugaban ƙasar Nijeriya ya ɗauka a lokacin gwamnatinsa a fannin man fetur, ya samar da sauƙi da kuma walwala ga al’ummar Nijeriya, sannan man ya wadata. Haka nan a ɓangaren wutar lantarki, da inganta harkokin ilmi da sufuri na motocin gwamnati a cikin sauƙi, da rage kuɗin makaranta, da inganta harkar lafiya da tsaro. Duk wannan an yi ne a saboda inganta rayuwar ɗan Nijeriya.
A yau mu tsaya mu kalli yadda Nijeriya take, shin abubuwan da suka faru a baya na tafiyar da mulki a Nijeriya, da waɗanda suke faruwa a yanzu, shin akwai bambanci a ciki ko babu? Sannan gaba muka ci ko baya muka ci? Duk da cewa kuɗin da gwamnati take tarawa na yanzu ya ninka wanda na gwamnatin Marigayi ‘Yar’adua da Goodluck Jonathan suka tara ninkin-ba-ninkin, amma me ya sa ‘yan Nijeriya suke shan wahala a yanzu?
Na farko akwai rashin iya shugabanci ga shugabanni biyun da suka zo bayan ‘Yar’adua da Goodluck Jonathan, su ne; Buhari da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na yanzu. Tsohon shugaban Nijeriya Buhari ya samu shinkafar ƙasar Thailand ana sayar da ita N7,500 babban buhu mai nauyin kg 50, yayin da ƙaramin buhu 25kg a kan N3,300. Haka nan Buhun sugar baya wuce N10,000, filawa N4,500 katon ɗin taliya silɓer N2,400 taliyar ɗangote N1,500 da N1,600 haka Macaroni da sauransu.
Sannan mu sani cewa, shinkafar ƙasar Thailand ko Indiya, ko ta Ingila da sauran ƙasashen da suke shigo mana da shinkafa ko taliya da sauran kayayyaki, idan aka ɗoro su a jirgin ruwa sai sun ɗauki lokaci kafin su iso Nijeriya, bayan sun iso a biya kuɗin fito da na saukewa, sannan a sake lodawa a raba kasuwannin kudu da Arewa, amma farashin Thailand Rice bai wuce dubu bakwai da ɗari biyar ba.
To yau sai mu kalli shinkafarmu ta gida da ake nomawa a nan gida Nijeriya, a kuma gyarata a ɗura a buhu, nawa ake siyarwa a yanzu? Ana maganar Nairai dubu ɗari da ɗoriya ne kuɗin kowanne buhu, mai sauƙi-sauƙi ce za a same ta a N95,000. Kuma abin mamaki, duk inda ka shiga za ka ga kamfanunnikan shinkafar da manomanta, amma har yanzu wani talakan tafi ƙarfinsa sai dai yaci tuwo ko ya sha kunu.
Yadda al’amurra suka taɓarɓare a Nijeriya a yanzu, babu dalilin da zai sa mu ce an samu ci gaba, sai dai ci baya. Domin duk wani abu da yake samuwa a cikin sauƙi a baya ga ‘yan ƙasa, to yanzu da wahala yake samuwa, wani ma sai dai a haƙura dashi domin yafi ƙarfin talaka. Duk mai hankali da tunani, haɗi da bibiyar halin da al’amurra suke wakana a ƙasar nan, ya tabbatar da cewa koma-baya a ka samu a cikin shekaru tara na mulkin Buhari da Tinubu, mumman koma-bayan da ya haifar da ƙaruwar cin hanci da rashawa, ayyukan ɓarna da sata, fashi da makami da bunƙasar ayyukan ta’addanci irin su; Garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fasa, kassara noma, rashin aikin yi ga ‘yan ƙasa, lalacewar ilimi, lalacewar kiwon lafiya, matsalar wutar lantarki, taɓarɓarewar tsaro, rashin kyawun hanyoyi.
Salon mulki marar ma’ana na tsohon shugaban ƙasa Buhari da Tinubu mai ci yanzu, ya gurgunta al’amurra da dama na ci gaban ƙasar nan. A yanzu an tara kuɗi a wannan gwamnatin, amma ba a magance matsalar tsaro ba, ana ƙara tara maƙudan kuɗi, amma abinci yana gagarar talakawa, ana ci gaba da tara kuɗi, amma kuma an gaza samar da sauƙi da walwala ga ‘yan ƙasa.
Kullum komai ƙara tashi yake, ilimi ya taɓarɓare, noma ya taɓarɓare sakamakon ayyukan ‘yan bindiga a mafi yawan yankunan da suke noma tuƙuru. Hasken wutar lantarki ya gagara samuwa ga ‘yan ƙasa, a cikin watanninsa na shugabanci, an yi ƙarin kuɗin man fetur sau huɗu, an ƙara haraji, an takura al’umma ta ko ina.
Yaran da basa zuwa makaranta sun ƙara yawa, mabarata sun ƙara yawa, ɓarayi sun ƙara yawa, ‘yan ta’adda sun ƙaru, karuwai sun ƙaru, ‘yan damfara sun ƙaru, mace-macen aure ya ƙaru, kisan gilla da ayyukan ɓata-gari sun ƙaru, cin hanci da rashawa ya ƙaru, satar kuɗin ƙasa ga ma’aikatan gwamnati ya ƙaru, rashin gaskiya da adalci a hukumomin ya ƙaru. Duk wata hanya da ɗan ƙasa zai samu sauƙin rayuwa an tosheta.
ɗan ƙasa yana samun walwala da sauƙin rayuwa ne ta hanyoyin gudanar da rayuwarsa cikin adalcin da gwamnati take yi masa, na samar da (welfare) a gare shi, ta yadda zai ci moriyar Dimokraɗiyya. A saka masa tallafi a wutar lantarki, tallafi a man fetur, tallafi a makaranta, tallafi a transportation, tallafi a harkar noma, tallafi a aikin Hajji, tallafi a ruwan sha, tallafi a kiwon lafiya da sauransu. Amma daga lokacin da gwamnati ta cire tallafi a irin waɗannan abubuwan da su ne ginshiƙai a ƙasa, to dole ne ‘yan ƙasa su tsinci kansu a cikin matsananciyar wahala da ƙuncin rayuwa.
Don haka, a nan za mu iya cewa ‘yan majalissun ƙasar nan duka ɓangarorin, tabbas! Ba sa kishin ƙasa da al’ummar ƙasa, haka nan a gwamnonin jihohi. Domin duk abinda shugaban ƙasa zai yi, tilas sai ya nemi ta bakin jagororin al’umma, kuma dole sai da amincewarsu zai iya aikata abinda yake so yayi a cikin ƙasa. Wannan ce ma tasa duk wani abu sai ya gabatar dashi gare su, suyi karatun farko suyi na biyu, sannan suyi karatu na ƙarshe kafin su saka hannu. To idan haka ne, me zai sa mu riƙa ganin laifin shugaban ƙasa kawai? Dole sai mun koma mun kalli ‘yan majalissunmu, Sanatoci da gwamnonin jihohinmu. Yau idan majalisa taso, to duk wasu sauye-sauyen shugaban ƙasa za su iya canza su idan suka nuna rashin amincewa. To amma da yake batu a ke na talakawan ƙasa, shi yasa hakan bai zamo damuwarsu ba. Amma duk lokacin da wani al’amari ya bijiro na ƙashin kansu, to za ka ga sun haɗa kai, suyi murya ɗaya, kuma su tsaya a kan abin har sai shugaban ƙasa ya aiwatar dashi.
Daga NAFI’U SALISU.
Marubuci/Manazarci, daga Kano Nijeriya. [email protected]
[email protected]. 08038981211-09056507471.
