Samar da wutar lantarki mallakar jihohi ne mafita

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A daidai lokacin da nake wannan rubutu, jama’a a jihohin arewacin ƙasar nan irinsu Filato, Bauchi, Gombe da Binuwai, har ma da wasu ɓangarori a Jihar Kano suna can suna murnar dawo da wutar lantarki da a fuskanci katsewar na kusan makonni, sakamakon dawowar wutar ranar Laraba da ta gabata, biyo bayan matsalar da aka samu a tashoshin lantarki na jihohin Benuwai da Enugu. A dalilin haka jihohin arewacin Nijeriya da dama sun shiga matsalar rashin wuta, wanda ya haifar da tsaiko wajen gudanar da harkokin kasuwanci, sana’o’i, walwalar al’umma, har ma da gudanar da ayyukan gwamnati a wasu matakai. 

Tun kusan kimanin misalin ƙarfe bakwai na maraice da aka fara dawo da wutar lantarki a wasu garuruwan, jama’a suka riƙa nuna murna da dawowar wutar. An ga wasu matasa da yara a bidiyo suna ta kaɗe-kaɗe a tituna da cikin anguwanni, domin farinciki da dawowar wutar lantarki. Abin da ke nuna lallai jama’a sun sha wahala, a dalilin rashin wuta, yayin da ayyuka da dama suka tsaya, a daidai lokacin da jama’a ke fama da matsin rayuwa. Mata a cikin gidaje da ke taimakawa mazajensu da ƙananan sana’o’in da suke gudanarwa, wanda ke buƙatar wutar lantarki don kayan da suke sayarwa su yi sanyi, an durƙusar da su. Haka nan akasarin sana’o’in da ake yi na kayan sanyi, kayan nama, kifi, da abinci, waɗanda ake adana su a firinji duk sun gagara, saboda rashin wuta. 

Ƙalilan ne masu sana’a suke iya sayen fetur su kunna janareto, don su gudanar da sana’o’in su. Wuraren da matsalar wutar ta fi tsamari su ne asibitoci, masana’antu, wuraren adana abinci da magunguna, bankuna, makarantu da tashoshin watsa labarai na rediyo da talabijin. A waɗannan kwanaki an jefa Arewa cikin duhu, da fargaba kan matsalar tsaro, sakamakon yadda aka samu ƙaruwar aikata laifuka a cikin waɗannan makonni.

Tsananin rashin wutar ya sa hatta wuraren ibada da ke haɗa kuɗi su sayi man fetur da za a sa a janareto a yi ibada, sun fara karɓar kuɗi suna yi wa mutane cajin wayoyinsu. Yayin da sauran masu cajin waya suka ƙara farashin kuɗin cajin da suke karɓa da Naira 100 har zuwa 300, suna ba da dalilin tsadar litar man fetur da suke saya. 

Kimanin jihohin Arewa 17 daga jihohi 19 dake yankin Arewa ne suka fuskanci wannan katsewar wutar lantarki, da suka haɗa da Sakkwato, Zamfara, Katsina, Kaduna, Filato, Bauchi, Gombe, Kano, Jigawa, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Kogi, Binuwai da Nasarawa. Kamfanonin rarraba wutar lantarki na JEDC mai kula da jihohin Filato, Bauchi, Gombe, da Binuwai, da kamfanin KAEDCO mai samar da wutar lantarki a jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da Kebbi, da kuma KEDCO mai ba da wutar lantarki a jihohin Kano, Katsina, da Jigawa. Harwayau, kamfanin AEDC mai kula da wutar lantarki a Abuja, Neja da Nasarawa, sun yi ta fitar da sanarwa a kafafen watsa labarai suna bai wa masu hulɗa da su a waɗannan jihohi haƙuri cewa sakamakon matsalar da aka samu. 

Bincike ya nuna cewa, tun da Gwamnatin Tarayya ta sayar da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta ƙasa (NEPA), an samu katsewar wutar lantarki a Babbar Cibiyar Samar da Wutar Lantarki ta ƙasa da ke Shiroro har sau 108. Tun da aka samu wannan katsewar wutar lantarki na baya-bayan nan a ranar 21 ga watan Oktoba, al’ummar Arewa suka shiga cikin ruɗani da damuwa, sakamakon rashin sanin takamaiman me yake faruwa. Sai bayan kimanin mako guda ne kafin aka samu sanarwa kan cewa an gano ‘yan ta’adda ne suka datse hanyoyin wutar lantarkin, kuma yankin da abin ya faru wuri ne mai haɗarin shiga, saboda dandazon ‘yan bindiga da ke wajen. 

An jiyo Ministan Kula da Wutar Lantarki Adebayo Adelabu yana danganta matsalar da ayyukan ‘yan ta’adda waɗanda suka datse hanyar wutar lantarki da ke tsakanin Shiroro zuwa Kaduna, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ya nuna damuwa da halin ruɗanin da aka shiga a ƙasa. Har ya ba da umarnin Babban Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaro da Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, da Babban Hafsan Sojojin ƙasa da na Sojojin Sama, su tabbatar an samar da tsaro ga injiniyoyin da za su yi aikin gyaran, domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa. 

Kodayake wani rahoton ya bayyana cewa, inda matsalar take yana tsakanin dajin Igumale ne a Jihar Binuwai, kusa da iyakar Jihar Inugu. Injiniyoyi a Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na TCN suka bayyana cewa, tilas sai an kai manyan kayan aikin gyaran hanya da jami’an tsaro, don a gyara hanyar da za a shiga dajin saboda caɓi da laka. 

A wata takardar ƙorafi da ƙungiyar Dattawan Arewa ta fitar da nufin nuna rashin jin daɗinta da halin da Arewa ta shiga, ta nuna rashin dacewa kan wariyar da ake nunawa Arewa a ɓangaren wutar lantarki. A ta bakin Kakakin ƙungiyar Farfesa Tukur Muhammad-Baba, bai kamata a ce Legas kaɗai tana da ƙananan cibiyoyin wutar lantarki har 8, amma a Arewa gaba ɗaya 3 ake da su kaɗai, a Jos, Kaduna and Kano. Alhalin daga Arewa ake samar da wutar lantarkin. Sun nemi lallai a samar da hanyoyin da za a inganta wutar lantarki a Arewa, domin farfaɗo da masana’antu da kasuwanci, da sauran harkokin cigaba da kullum suke samun komabaya. 

An daɗe ana zargin maƙarƙashiya tsakanin Arewa da Kudu, musamman a ɓangaren makamashi da wutar lantarki, wanda dalilin haka ya janyo durƙushewar masana’antu a Arewa, da bunƙasar masana’antun Kudu. 

A jawabin da Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya take yi na samar da wata hanya ta inganta wutar lantarki ta amfani da hasken rana a kowacce jiha, inda ake shirin samar da na’urorin tattara wutar lantarki daga hasken rana mai ƙarfin Megawatt 100, domin rage dogaro da Babbar Cibiyar Samar da Wutar Lantarki ta ƙasa. 

Bayan samun nasarar gyaran wutar, Kakakin Kamfanin Raba Wutar Lantarki na ƙasa, TCN Ndidi Mbah ya ce an samu nasarar dawo da wutar lantarki a wasu jihohi ne bayan gyaran da aka yi wa Cibiyar Samar da Wutar Lantarki mai ƙarfin 330 Kɓ da ke tsakanin Ugwuaji zuwa Apir, yayin da ake kan aiki a ɗaya ɓangaren babban layin wutar da ya bi ta Apir zuwa Lafiya. Ya ƙara da cewa, wannan gyara ne aka yi na wucin gadi kafin a kammala ainihin gyaran shiyyar bakiɗaya.

Tuni dama gwamnatocin wasu jihohin a Arewa sun fara shirin samar da nasu kamfanonin samar da wuyar lantarki na cikin gida, da nufin inganta samar da makamashi ga jama’arsu, bunƙasa masana’antu da kasuwanci. Daga cikinsu akwai Jihar Neja, wacce ke ƙarƙashin Kamfanin AEDC, inda Gwamnan jihar Umaru Bago ya ƙaddamar da wani shiri da aka yi wa laƙabi ‘A Haskaka Neja’, wato ‘Light Up Niger’ a Turance. 

Ya kamata gwamnonin jihohin Arewa su tashi tsaye su tabbatar sun samar wa jihohinsu hanyoyin samar da cigaban masana’antun zamani da bunƙasar tattalin arziki, a daina dogaro da Gwamnatin Tarayya. A zaƙulo ƙwararrun injiniyoyi da ake da su daga ‘yan Arewa ko ta haɗaka da kamfanoni masu zaman kansu, don inganta tsarin samar da wutar lantarki daga hasken rana a jihohinsu. Hakan zai bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga mata da matasa, farfaɗo da ƙananan masana’antu, da magance ƙalubalen tsaro.

By ukarofi