PRP reshen Katsina za ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan matsalar lantarki a Arewa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyar PRP, a Jihar Katsina, Alhaji Imrana Jabiru Jino ya ce zai maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan tsawon kwanakin da aka ɗauka ba wutar lantarki a Arewacin Nijeriya.

Ya ce ya shirya tattara bayanai tare da aika su ta yanar gizo ga duk iyalan mutanen da suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu sanadiyyar ɗaukewar wutar lantarki.

Jino ya koka kan yadda manyan kamfanoni da ƙananan ‘yan kasuwa suka tafka asara sanadiyyar rashin wutar lantarki.

“ƙananan ‘yan kasuwa da suka haɗa da masu walda, aski, sayar da kayan sanyi da sauransu da suka yi asara da marasa lafiya waɗanda aka sanya masu na’urar shaƙar iska da suma suka gamu da ɗauke wuta,” inji Jino.

Tsohon ɗan takarar ƙarƙashin gidauniyarsa mai suna Gidauniyar Jino, ya ce da zarar sun kammala haɗa takardun masu ƙorafe-ƙorafe, zai shigar da ƙara na neman biyan diyya.

Shugaban gidauniyar ya kuma nuna takaicinsa kan yadda masu riƙe da madafun iko da sarakuna, malamai na Arewacin ƙasar suka zuba inda al’ummar yankin ke shan wahala.