Yanzu ake ganin irin nasarar jajircewar da NEPU ta yi kan talaka – Farfesa Kamilu Fagge

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An gudanar da taro karo na bakwai a kan ranar tunawa da kafa Jam’iyyar NEPU shekaru 73 da suka gabata da cibiyar nazarin dimukraɗiyya ta Jami’ar Bayero ta gudanar a gidan Mumbayya a ranar Talata.

Da yake gabatar da jawabi a yayin taron, Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana cewa siyasar aƙida ce ke biyan buqatun jama’a, duk da jam’iyyar NEPU ba ta kafa gwamnati ba amma ta tsaya ta jajirce da yanzu ake ganin nasarar da ta cimma.

Ya ce dagewar da NEPU ta yi ne ta ƙwato wa talaka ‘yancinsa, yanzu abubuwan da ta yaƙa, misali a tsarin ƙananan hukumomi an ɗabbaƙa shi a ƙasa, duk da ba ita take gudanar da mulki ba.

Amma gwagwarmaya da ta yi ta ƙwatowa ɗan talaka ‘yanci, yanzu fiye da kashi 70 ko 90 na masu mulki ‘ya’yan talaka ne.

Ya ƙara da cewa, “ba don irin wannan gwagwarmayar ba, ‘ya’yan talakawa ba za su samu damar har su shiga a dama da su kamar yadda ake yanzu ba a mulki.”

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya yi nuni da yadda a yanzu kuma al’amura suka tavarvare fiye da na da yadda aka yi gwagwarmaya a baya, a ga an canza lamarin. Don yanzu ma haka ya kamata a yi a yanzu mutane kada ja hannunsu su zauna, fitowa za su yi su dage su ga cewa sun zaɓi shugabanni amintattu an kafa gwamnati mai adalci da za ta biya buƙatun al’umma.

Farfesa Kamilu Sani ya ce, “yin irin wannan fafutuka sai an ɗauke kwaɗayi da ƙin a yi amfani da kuɗi a juya ra’ayin mutane, sannan kuma sai mutane sun kashe kasala kar su gajiya wajen zaɓen shugabanni nagari. In ana so a kawo canji, dama damar a hannun jama’a take, don talakawa sune ke da ‘yanci da iko su iya canza irin wannan al’amari, ba su naɗe hannu kawai suna jira abubuwa su canza don kansu ba, dole sai an jajirce ta yin abinda ya kamata kamar yadda ‘yan NEPU suka yi.”

Shi ma mai masaukin baqin taron Daraktan Cibiyar Nazarin Dimukraɗiyya na gidan Mumbayya, Farfesa Habu Muhammad Fagge da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce yanzu an samu kai a ƙasa irin ta Nijeriya mai arziƙi, amma talauci ya dabaibaye mutane, waɗanda suka kaɗa ƙuri’a su sun yi ne da zimmar cewa, za a ceto su daga ƙangin da suke ciki, amma aka samu akasi talauci daɗa katutu yake ma.

Ya ce yanzu abubuwan rayuwa na havaka yana kuma guje wa talaka, yana shiga matsi, amma kuma su masu madafun mulki abubuwan rayuwa ne ke daɗa bunƙasa a gare su, hakan ya tabbatar da cewa siyasa ta aƙida irin ta NEPU da aka yi yanzu babu irinta, sai dai a yi ƙoƙarin yadda za a ja hankalin mutane su karkata wajen yadda za a yi gyara a daidaita bakin zaren.

Habu Muhammad Fagge ya yi nuni da cewa yadda za a gyara bakin zaren ana buƙatar su kansu jam’iyyu ya kasance ba a yaudari masu zaɓe ba, su kuma masu zaɓe ba su yaudari kansu ba.

“Mu zaɓi mutum nagari na kowa, da aka riga aka san aƙida da yake da ita kaɗai za ta iya canza alƙibla na talaka.”

Ya ce su kuma jam’iyyu ya kasance sun ɗauki abinda ake buqatar a ga suna yi, shi ne faɗakarwa, domin yawa-yawan jam’iyyu ba sa faɗakarwa, domin in suka faɗakar ta ya ya za a yi su yaudari jama’a. Rashin yin hakan sai ga shi an samu ƙungiyoyin sa kai ne suke faɗakarwar, wanda jam’iyyu ne ya kamata su yi, sannan idan jam’iyya za ta faɗakar, fadakarwar ta gyara ne.

Amma jam’iyyun da yawansu ba hakan suke ba, sai dai kurum akai mutane cikin duhu, a zo ka yi zaɓe yau, a ranar da aka rantsar da mutum, sai ya faɗi wani abu da daidai yake da ya kashe rayuwar talaka.

Farfesa Habu Fagge ya ƙara da cewa suma ‘yan jarida haƙƙin su ne su faɗakar domin mutane su fahimta cewa aƙida da tsari irin na jam’iyyu aiwatar da shi shine abinda ya kamata a yi a wannan lokaci, domin a kawo canji.

Ya bada misali da cewa ƙasashe da suka cigaba a dimukraɗiyya su, idan ka ce za ka yi a,b da c idan ka zo ka samu Gwamnati bakayi a,b,c ba ka tafi kana z,d da f, to ka shiga a uku, babu ma wanda zai daxa zaɓenka, amma anan a yayinda kazo kayi siyasa ta kuɗi, za a zo a zaɓe ka.

“Da mu da jam’iyyu ana buƙatar canji sai anyi karatun ta natsu dan a kawo gyara ga qasa in ana buqatar dimukraɗiyya ta ɗoru a kan doro na gyara na canji.

Farfesa Habu Muhammad Fagge ya ce akwai yaqinin ƙasar nan na da arziƙi da dukkan maƙotanta basuda irinsa ,amma babban abinda yake faruwa jagoranci ya yi mana wuya wala’alla baragurbin shugabanni muke zaɓa, to ya kamata wajen fitar da shugabanni mu tsaya mu zaɓi mutane ba ‘yan jari hujja ba, waɗanda za su kaimu ga tashar naƙi, da za su kai mu ga cigaba da za su canza rayuwarmu ta inganta ba tare da nuna ƙabilanci ko bambanci na launi ko ɓangaranci ba, ƙasar za a sa a gaba ayi abu saboda Allah a aiwatar da abinda aka faɗa, ba yaudara ba, waɗannan abubuwa matakai ne in aka yi amfani da su kuma mu yi iƙirarin cewa, duk jam’iyyar da ba ta aiwatar da da duk abinda tasa a gaba na alheri ba, a dawo a yi waiwaye in an zo zaɓe kar a zaɓi ɗan takarar da ta tsayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *