Yanzu-yanzu: Oyebanji na APC ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Gwamna Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka gudanar a ranar Asabar.

Babbar jami’ar zaɓen jihar, Adenike Oladiji ta sanar da haka a ranar Lahadi yayin bayyana sakamakon zaɓen, inda ya ce Oyebanji ya samu ƙuri’a 319,224.

A cewar Oladiji, ɗan takara jam’iyyar PDP, Oluwole Oluyede, ya samu ƙuri’a 40,543, yayin da Dare Bejide na ADC ya samu gusa 12,872.

Ta ce, jimillar ƙuri’u 384,940 ne aka tantance a zaɓen, inda aka samu sahihai guda 375,777, sai 6,332 da aka soke su.

An fara zaɓen ne da misalin ƙarfe 8:31 na safe inda kuma aka kammala da ƙarfe 2:30 na ranar, wanda sama da masu zaɓe guda 300,000 suka shiga daga ƙananan hukumomi 16 na faɗin jihar.

An zaɓi Oyebanji mai shekaru 58 ne a matsayin gwamna a ranar 18 ga Yunin 2022. Ya kuma karɓi ragamar aiki ne a Oktoban shekarar.

Zaɓen na 2026 ya sa Oyebanji zama gwamna mai ci na farko a tarihin jihar ya sake lashe zaɓen kujerar gwamnan.

By Babaji

Leave a Reply