Yawancin auren dole da ake yi wa yara ana gina shi ne bisa son zuciya da kwaɗayi – Lantana Jafar

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A wannan satin shafin Gimbiya ya karɓi baƙuncin mata guda biyu, waɗanda suka kasance fitattu kan sha’anin bayar da gudunmuwa a ɓangaren tarbiyya da kuma zamantakewar aure.
Dalilin gayyatar tasu dai ba ɓoyayye ba ne, kasancewar shafin namu na duba ne kawai ga bukatun uwayen gida, hanyoyin da za su bi kan gyara zamantakewar su ta aure ko zaman gida, zuwa ga tarbiyyar ‘ya’yansu da kuma zaburarwa kan neman na kai.
Baƙin namu za su amsa mana tambayoyi ne kan ɗaya daga cikin matsalolin da ke ciwa ƙasar Hausa ko in ce mata tuwo a ƙwarya, wato matsalar auren dole, wadda har kawowa yanzu da ake ikirarin kai ya waye ba a samu shawo kan matsalar auren dole a tsakanin al’umma ba.

Kada in cika ku da surutu, ku gyara zama, ku bayar da hankalinku don kwasar darussan da ke cikin wannan tattaunawa. Kamar kullum, Aisha Asas ce tare da Lantana Jafar da kuma Jamila Abdullahi R.Lemo.

MANHAJA: Assalamu alaikum. Muna yi wa baƙinmu barka da zuwa wannan shafi na Gimbiya.
JAMILA: Amin wa alaiki salam. Barkanmu dai.
LANTANA: Wa’alaikum salam. Barkanmu.

Bari mu fara da ke Jamila, za mu so ki yi mana bayanin auren dole.
JAMILA: Ataƙaice, auren dole wani haɗi ne da iyaye ko kakanni zuwa shaƙiƙan ‘yan uwa suke haɗawa su ƙulla a tsakanin mutum biyu; mace da namiji, wala ya’alla cikin dangi ko akasin haka, kuma bisa rashin duba da so da ƙauna da yarda, ballantana wata maganar fahimtar juna da shaƙuwa a tsakanin waɗanda za a zargawa auren dolen.

Gare ki ‘yar uwa Lantana, za mu so ki mana ƙarin haske kan auren dole.
LANTANA: A gaskiya yawancin auren dolen da ake yi wa yara ana gina shi ne a bisa son zuciya da kwaɗayin abin da za a samu na ƙyale-ƙyalen arzikin duniya.
Yawanci iyaye suna amfani da damar da Allah ya ba su a matsayinsu na mahaifa, domin cimma burin su. Da yawa basa duba makomar rayuwar ‘ya’yansu bayan aura masu wanda basa so. Wanda hakan na haifar da babban matsala a rayuwar ‘ya mace.

Sis Jamila, ya ake kallon auren dole a ƙasar Hausa?

To, bisa fahimtata irin wannan aure na dole a ƙasar Hausa, mafi yawa sun san cewa sam bai kyautu ba, duba da irin tarin matsalolin da yake haifarwa a cikin al’ummar Hausawa, sakamakon cewa da yawa idan an yi yunqurin yin sa, ba ya haifar da ɗa mai ido dangane da abin da yake janyowa na kassara rayuwa da taɓarɓarewa, ko kuma abin da yake biyo baya idan an sami nasarar yin sa bisa tilas.

Sis Lantana, wasu na yawan danganta auren dole da Hausawa kawai. Shin ko a ƙasar Hausa ne kawai ake yin auren dole?
Gaskiya ba iya ƙasar Hausa ba ne kaɗai a ke auren dole ba. Abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya.

Sis Jamila, A da can iyaye sun fi yi wa ‘ya’yansu auren haɗi ba tare da ma wasu sun san juna ba. Wannan auren ne ake kafa hujja da shi a yanzu ga waɗanda ke yi wa ‘ya’yansu auren dole. Shin ko akwai bambanci tsakanin wancan auren da kuma irin wanda ake yi yanzu?
Matuƙa da gaske: dalili, akwai batun ɗabi’a da ilimi da kuma wayewa waɗanda suka sha bamban wajen taka rawar gani a da da kuma yanzu, musamman idan muka yi duba da zamani.
Na farko; ɗa’a da kunya da yakana da sanin darajar na gaba, ballantana dungurugum iyaye, mutanen da sun sha bamban da na yanzu shi ya sa aka yi nasarar yi musu auren dole da kika faɗa wanda ake kafa hujja da shi.
Na biyu; rashin ilimi sosai ko mai zurfi ya taimaka wajen danƙwafar da mutanen da tare da daƙile sun da aka riƙa yi ana yi masu auren dole su zauna daram sakamakon rashin sanin kansu da haƙƙoƙinsu.
Na uku; duhun kai da rashin wayewa su ma sun taimaka wajen rashin sanin ‘yancin kansu na abin da suke da iko a kai game da shirya burukan da zai inganta ko gina rayuwarsu, musamman ta fuskar samun rayuwar zamantakewar aure mai cike da annushuwa da nishadi da kuma jin dadi, ba wai kawai buƙatar a yi auren a wuce wajen ba.
Saboda haka, idan kika kalli waɗannan batun da na kawo tare da zamanin da muke ciki. Ta yaya kike ganin za a yi wa ‘ya’yan yau irin wancan aure a kwashe lafiya, bayan sun san cewa su ma mutane ne masu haƙƙi da ‘yanci a rayuwarsu bisa tsarin Allah da koyarwar manzo SAW? Baya ga kuma halin rikau ɗin mutanen yanzu da tarbiyya sai a hankali, a kan daidai ma ya aka ƙare da mutanen yanzu ballantana kuma an tauye haƙƙinsu?

Sis Lantana, ko akwai wani alfanun da ke cikin auren dole?
Kwata-kwata babu wani alfanu a tattare da auren dole. Domin ya na haifar da koma baya a rayuwar ɗan adam. Sannan yana kashe burin da ke cikin zukatan mutane.

Sis Jamila, za mu so jin wasu dalilai da ke sa iyaye yiwa ‘ya’yansu auren dole.
Bisa fahimtata a yanzu dai ina ganin akwai ire-iren waɗannan batutuwan:
1- Auren jari; ƙila saboda zalama da kwaɗayin abin duniya.
2- Son rai ko na ce zuciya; bisa wani ra’ayi can daban na iyaye ko dangi, mara hujja da tushe.
3- Rashin haquri da ƙaddarar rashin samun miji da wuri; wannan yana sa wasu iyayen yi wa ‘ya’yansu auren dole ta hanyar haɗa su da wani ko ‘yar ba ta so.
4- Mutumci da cancanta ta hanyar yabawa da nagartar mutum; wasu iyayen kan yi amfani da wannan dama su yi wa ‘ya’yansu auren dole ko ba sa son mutum.
5- Rashin kamun kai ga ‘ya mace, musamman idan ta ɗauko hanyar lalacewa tana bin maza; iyaye kan yi wa ‘ya auren tilas gudun jawo musu abin kunya.
6- Kunya da kara; idan aka yi katari da ɗan uwa na kusa da ke son yarinya, koda ba ta son shi iyaye kan rufe ido su yi mata tilas su aura masa ita ta hanyar fake wa da auren zumunci.

Harwayau dai muna kanki Sis Jamila, a cikin dalilan da ki ka ambata waɗanne ne za a iya cewa sun dace da yi wa mace auren dole?
Anya kuwa? Gaskiya a fahimtata babu dalili, kowace cuta tana da magani matuƙar za a yi hakuri a bi tafarkin Allah, Hausawa ma sun ce da muguwar rawa gwamma ƙin tashi.

Wasu na ganin yi wa mace auren dole bai cika matsala ba, abinda suke gani namiji ne kawai bai kamaci a yi masa auren dole ba. Sis Lantana me za ki ce game da wannan?
E, to zan iya amincewa da hakan, mace na iya haquri ta zauna da wanda bata so a bisa bin umurnin iyaye. Saɓanin namiji wanda bai da hakuri da juriya irin na mace.

Za mu so jin ra’ayin ki kan wannan tambayar, sis Jamila.
Tirka-tirka ke nan. Kowane ɓangare babu dadi, amma dai duba da yanayin rauni na ɗiya mace, takan jure ta daure wa auren dole, musamman idan aka dace ita ɗin ta sami tarbiyya sosai ta addini.
Shi kuwa namiji idan aka hada shi da wadda ba ya so, koda ya yi ta maza ya karɓa, gaskiyar magana mafi yawan irin waɗannan mata suna shan kuɗarsu a wajen mazajen ta ruwan sanyi, domin su kaɗai su kan san irin wulaƙanci da cin fuskar da suke fuskanta a wajejen mazajen; ta mahaukaci da ya ci kashi, ya ce abin ba dadi.

Sis Jamila, Waxanne illoli ne auren dole ke kawowa ga lafiyar macen da aka yi wa shi?
Na farko akwai:
1- Rashin kwanciyar hankali da walwala da sukuni.
2- Daga nan sai cutar muntukus ( depression ) kowa dai ya san irin illar wannan cuta ta zunzurutun tsananin bakin ciki da damuwa da take haifar da ita, shi ke nan ta ƙulla abota ta sunturin ganin likita da shaye-shayen ƙwayoyin magani.
3- ɗaukewar sha’awar mace bisa rashin son mijin, tunda ba shi take muradi ba, saboda an haifar mata da ƙunci a cikin rayuwa.
4- Sannan mace takan iya haɗuwa da matsalar yoyon fitsari, sakamakon tirsasa ta da mijin yake mata ta hanyar yin jima’i da ita ta qarfi da yaji, tunda ba shi take so ba, daga ƙarshe tai ta fama da larurar, idan ba a dace da magani ba shi ke nan rayuwar ta tagayyara kacokan.
5- Jefa mace a halaka, idan aka yi rashi dacewa da ƙarfin imani da tsoran Allah su sa ta kashe mijin. ( Wa’iyazu billah ) Allah Ya kiyashe mu, amin. Daga nan ƙwaƙwalwa kuma ta sami matsala ke nan.

Sis Lantana ko akwai wani ƙarin bayani da za ki yi akan wannan?
A wannan tambayar za mu dasa aya, wadda da yardar mai dukka za mu soma da samarwa masu karatunmu amsar ta, kafin wasu tambayoyin su biyo baya, waɗanda muke da tabbacin za su amfani masu karatu.
Ku nemi Blueprint Manhaja ta mako mai zuwa don jin ci gaban firar.

By ukarofi