Yawan karatun littattafan marubutan Nijeriya ne ya sanya na goge a rubutun Hausa – Ikilima Adam

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ikilima Adam ɗaya ce daga cikin marubutan adabin Hausa da ake da su a maƙwaftan Nijeriya. Duk da kasancewarta ‘yar ƙasar Jamhuriyar Benin, wacce ta ke rayuwa a cikin harshen Faranshi, amma da wuya mai karatu ya fahimci haka a cikin rubuce-rubucen da take yi, saboda yadda ta saje da marubutan ƙasar Hausa. Sannan ita kaɗai ce a tarihin rubutun Hausa da aka samu matashiyar mace ta shirya gasar rubutun gajeren labari da bai wa marubuta damar baje basirarsu kan matsalolin rabuwar aure. Iqilima, wacce ta kafa Gidauniyar Tallafawa Harkokin Adabi ta Kyauta Daga Allah Foundation na da burin ganin marubuta sun hada kansu kuma sun jajirce wajen neman ilimi da fadakarwa ga al’umma. A tattaunawar da ta yi da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa sha’awar da take da ita na zama gogaggiyar marubuciyar labaran finafinan Hausa. A sha karatu lafiya!

MANHAJA: Ina son ki fara da gabatar mana da kanki.

IQILIMA ADAM: Assalamu alaikum. Sunana Iqilima Adam wacce aka fi sani da Kyauta Daga Allah. Ni marubuciya ce, ƴarkasuwa, kuma uwa.

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taqaice?

Ni dai asalina haifaffiyar garin Kwatano ce a Jamhuriyar Benin, maƙwafciyar Nijeriya daga gabas. A nan na taso har zuwa girmana, kuma har na yi aure. Yanzu haka ina da yara uku, biyu maza ɗaya mace. A ɓangaren karatu kuma, na yi karatun boko da na addini, har zuwa matakin da nake a yanzu.

Wanne abu ne ya faru a rayuwarki lokacin tasowarki wanda ya taimaka wajen inganta tarbiyyarki da tunaninki?
Kulawar da na samu daga iyayena da yayyena. Tabbas sun zama min tsani a rayuwata, don kuwa ta silarsu ne rayuwata ta inganta sosai har kawo yanzu.

Wanne abu ne ya sa ki ka fara sha’awar rubutun adabi?
Yawan karance-karancen littattafan Hausa yana ɗaya daga cikin abin da ya sanya min sha’awar yin rubutu, domin ni ma in isar da nawa saƙon har zuwa inda nake so ya je.

Ko za ki iya tuna labarin farko da ki ka fara rubutawa?
Labarin farko da na fara rubutawa shi ne ‘Kai Ka Jawa Kanka.’

Wane ne ya fara koya miki yadda za ki yi rubutu, ko nuna miki ƙa’idojin rubutu?
A gaskiya babu wanda ya koya min yadda zan yi rubutu, tun da na yanke a zuciyata zan yi rubutu sai kawai na fara. Malamina a fagen rubutu, Jibrin Adamu Jibrin Rano shi ne zan ce ya qara buɗe min ido a kan dabarun rubutu da sanin ƙa’idojinsa, ta dalilin Aji Na Musamman da ya bude a manhajar WhatsApp. Sai kuma aminiyata a cikin marubuta dake ɗan taimaka min a inda ban gane ba, ko kuma a inda ta ga na yi wani kuskure, sai ta gyara min. Daga nan nima na riƙe kenan.

Wacce shekara ki ka fara fitar da rubutunki kuma kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?
Rubutuna ya fara fita ne tun a shekarar 2019, yanzu haka littattafaina sun kai biyar, sai kuma wanda muka yi na haɗaka da wasu marubuta.

Gaya mana sunayen littattafanki, kuma ki yi mana bitar fitattu uku a cikinsu.
Na rubuta, ‘Kai Ka Jawa Kanka’, ‘ƙanwata’, ‘Rai ɗaya’, ‘Ruɗani’, da kuma ‘Makauniyar Shari’a’.
Labarin ‘Kai Ka jawa Kanka’, labari ne da yake nuni kan irin mugun sakacin nan da wasu iyaye maza suke yi, wajen bai wa ‘ya’yansu tarbiyya. Kamar yadda labarin ya zo akan wani mutum mai suna Khalid Sani wanda yake jarrabar aure-auren mata, inda har ya haifi mata goma sha biyu. Sai dai kuma dukkansu yana aurensu ne ba tare da ya kusance su ba. Sai dai ya gayyato wani daga waje ya je ya biya wa matarsa buqata a matsayin shi ne da kansa. Da zarar matar ta fahimci abin da ke faruwa, sai ya sa a kasheta, don kar ta tona masa asiri. A haka ya yi ta aure-auren matan suna mutuwa, sai da ya auro ta sha biyun ne aka samu tangarɗa.
‘Ƙanwata’ kuwa labari ne da ya shafi yaya da ƙanwa, wanda kuma suka fito ciki ɗaya. Sam ita ƙanwar bata ƙaunar yayarta, don tsabar ƙiyayya ma har guba ta sanya mata a abinci, domin ta mutu ta auri mijin ko kuma kowa ya rasa a cikin su. Har a ranar ɗaurin auren yayarta ta ƙulla makircin da mijin da za ta aura ya je cikin taron auren ya ce ya fasa ba ya sonta. Ɓacin ran yadda aka yi abin ya sa ɗan sarkin garin ya ce a mayar da auren kansa, daga nan kuma sabuwar dambarwa ta tashi.
Sai littafin, Rai ɗaya Jan Zaki, labarin Aliyu Haidar wanda rayuwarsa take cikin mugun hatsari, sakamakon magautan mahaifinsa suna neman sa su kashe, dalilin haka ya sanya yake rayuwa cikin wani kogo shi da iyayensa. Labarin dai yana nuna yadda masu kudi suke raina talaka ko ƙyamatarsa, a rashin sanin wanda suke wulaƙantarwa su ne ma silar arziƙinsu. Da kuma batun yadda kishiya ta ɗauki ɗan kishiyarta ta fitar da shi wata ƙasa, domin tsabar baƙincikin rashin haihuwar da Allah bai bata ba.

Shin kin taɓa buga wani a cikin littattafanki ko duka a onlayin ki ke sakewa?
Babu wanda na buga, duk na onlayin ne. Amma in sha Allahu, ina da niyyar bugawa nan ba da daɗewa ba.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako ƙungiyar ke miki a rubuce-rubucenki?
A halin yanzu dai, babu wata ƙungiya da nake yi, sai dai a baya na kasance mamba a ƙungiyar Jarumai Writers Association. Babu shakka zama cikin ƙungiyar ya sa na haɗu da marubuta da dama waɗanda muke alaƙa ta zumunci sosai da su har gobe, muna kuma bai wa juna shawarwari. Shugabar ƙungiyar wata jajirtacciyar mata ce ƙwarai, wacce ta riƙa matsawa ganin na yi rubutu, duk da a lokacin gaskiya bani da ra’ayin rubutun sosai.

Waye a cikin marubuta ya zama miki madubin kwaikwayo a salon rubutunsa ko gogewarsa?
Babu shakka ina alfahari da Aysha Aliyu Garkuwa, sanadinta na goge da harkar rubuce-rubuce sosai.

Yaya alaƙarki take da masu bibiyar littattafanki, kuma ta yaya ki ke hulɗa da su?
Ina da kyakkyawar alaqa da su, domin duk kiran da ake yawan yi min, don sharhi akan littattafaina ba na gajiyawa wajen saurarensu har mu taɓa hira kamar mun san juna. Ina jin daɗin hakan sosai.

Shin wani makarancin littattafanki ya taɓa baki wata shawara da ta sa har ki ka canza wani tsari da ki ka yi wa labarinki?
E, lokacin da nake rubuta labarin ‘Kai Ka Jawa Kanka’ lokacin da na zo qarshen labarin ina son na warware wani abu da ya shafi addini, akwai waɗanda suka bani shawara, saboda nazarin da nake yi, kafin na yanke hukunci kan yadda labarin zai qare. Saboda rubutun ba iya nan zai tsaya ba. Kuma na ɗauki shawararsu na canza yadda na so ɗin.

Yaya ki ke samun jigo ko basirar yin rubutunki?
Yawanci sai ina cikin damuwa ko kuma na ji wani abinda ya faru wanda ya taɓa ni, ko kuma ina zaune ni kadai sai wata basirar ta zo min.

Wanne littafi ne rubutunsa ya fi baki wahala, kuma wanne ne ya fi miki saukin kammalawa, mene ne dalili?
A gaskiya littafin ‘Kai Ka Jawa Kanka’ shi ya fi bani wahala wajen rubutawa, saboda a lokacin ina sabuwa a rubutu, sai kaina ya kulle matuka.
Littafin ‘Makauniyar Shari’a’ kuwa shi ne littafin da na kammala cike da jindaɗi, domin farkon da ƙarshen duk a tsare na yi su.

Yaya harkar rubutun adabi take a Jamhuriyar Benin, musamman yankinku na Kwatano, akwai marubuta sosai ko ƙungiyoyin marubuta?
To, ni dai a nan qasar ko a yankin Kwatano, zan iya cewa ni kaɗai ce marubuciyar adabin Hausa babu wasu marubuta da na sani.

Yaya ki ka koyi rubutu da Hausar Ingilishi a maimakon turancin Faranshi da ku ke amfani da shi a ƙasarku, har ga shi kin zama marubuciya?
Yawan karance-karancen littattafan da marubutan Nijeriya suke yi ne ya sanya na goge a rubutun Hausa da irin naku salon ingilishin na Birtaniya.

Su waye aminanki da ku ke zumunci sosai a cikin marubuta?
Ina zumunci da marubuta da dama, amma aminaina biyu ne, Sarat Alqasim (Maman Nusaiba) da Khadija Salisu Ibrahim (Maman Amatullah). Dukkansu ƙawayena ne tun a ƙungiyar Jarumai Writers Association.

Shin tun bayan fara rubutunki na kanki, kina samun damar karanta littattafan wasu marubutan?
E, ina karatu sosai.

A baya kin taɓa shirya wata gasar rubutun gajeren labari, ƙarƙashin gidauniyarki, me ya ƙarfafa miki gwiwa ki ka shirya wannan gasa, kuma a kan mene ne aka shirya?
Na sanya wannan gasa ne domin zaburar da marubuta da ƙarfafa musu gwiwa, da kuma ƙara inganta rubutun adabi. Sannan an sanya gasar ne akan illolin yawan mace-macen aure.

An ce ke kaɗai ki ka ɗauki nauyin ba da kyaututtukan kudi a gasar, wacce shawara za ki ba sauran marubuta kan irin haka?
E, tabbas ni kadai na ɗauki nauyin bayar da kyaututtukan har ma da na Alƙalan gasar. Kuma ina mai ba su shawara da in sun samu dama irin tawa su riƙa sanya gasar a tsakanin marubuta lokaci zuwa lokaci. Ba lallai sai wani hamshaƙin maiƙudi ko kamfani ba, komai ƙanƙantar abin da za a bayar zai qarfafawa wasu gwiwa.

Su waye suka taimaka miki wajen gudanar da wannan gasa, da ba da shawarwari?
A gaskiya ba zan manta da halaccin da Zakin Marubuta Ayuba Muhammad ɗanzaki, da Jibrin Adamu Jibrin Rano (Abu Amrah) da Bamai Dabuwa suka nuna min ba, a lokacin gudanar da wannan gasa. Sun taimaka min ƙwarai da gaske.

Wanne buri ki ke da shi nan gaba a harkar rubutun adabi?
Ina da burin ganin na zama marubuciyar finafinai, in sha Allah.

Mene ne shawararki ga sauran marubutan Hausa bakiɗaya?
Ina ba su shawara da su riƙa yawan karance-karance, domin hakan zai ƙara musu basira da cigaba a rubutun da suke yi.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Barewa bata gudu ɗanta ya yi rarrafe!

Masha Allah. Na gode
Alhamdulillahi. Ni ma na gode.