
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba zata yi tattaunawar sulhu da ƴan bindigar da suka addabi zaman lafiya a Jihar ba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wani tattakin neman zaman lafiya da wasu matasa suka shirya a Jihar inda ya ce suna cigaba da ƙoƙarin bin hanyoyin da suka dace wajen ganin an samu zaman lafiya a dukkan sassan Jihar.
Gwamnan ya kuma yaba wa matasan da suka shirya tattakin yayin da ake gudanar da bikin demokradiyya inda yayi kira da su bada gudunmawa wajen tabbatar da an samu zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar ta hanyoyin da suka dace.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, gwamnan yace sun samu cigaba a ɓangarorin magance matsalolin tsaro da bunƙasa harkokin ilimi da harkokin noma da na kiwon lafiya da inganta al’umma da sauransu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnatinsa ta yi nasarar ƙaddamar da biyan naira dubu 30 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Jihar a madadin dubu 7 da ta saba biya.
