Ƙaruwar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta

Spread the love

A cikin watan Yunin 2013, Hukumar Kula da Ilimi, Zamantakewa da Al’adu ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNESCO), ta sanar da cewa, Nijeriya ta zama ƙasa mafi yawan al’umma a duniya da ke da yara miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta.

Sauran ƙasashen da aka bayyana sunayensu a cikin rahoton sun hada da: Pakistan masu yara miliyan 5.1m marasa zuwa makaranta, Ethiopia 2.4, Indiya 2.3, da sauransu. A shekarar 2018, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta mayar da adadin zuwa miliyan 12.5, inda aka ɗora alhakin ƙaruwar hakan da hare-haren ta’addanci ga makarantu a Arewa. Duk da alƙawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na ƙara kuɗin tallafin ilimi da kashi 50 cikin 100 nan da shekarar 2023 da kuma kashi 100 nan da shekarar 2025, alƙaluman da aka samu a halin yanzu ya nuna cewa lamarin ya kau.

Akwai binciken da ke nuna cewa, daga nan har zuwa shekara ta 2030, za a cigaba da samun aƙalla kashi takwas cikin 100 na qananan yara da shekarunsu suka kai shiga firamare amma ba sa zuwa makaranta a yankin kudu da hamadar Sahara.

Shugabar Asusun Kula da Ilimin Yara na Majalisar ɗinkin Duniya, UNICEF, ofishin Jihar Kano, Rahama Farah, ta sanar a wata tattaunawa ta kafafen yada labarai kan ilimin ’ya’ya mata a ƙarƙashin shirin UNICEF na koyar da yara mata na 3 cewa, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya yanzu ya kai miliyan 18.5. A cikin wannan, miliyan 10 mata ne.

Nijeriya na buƙatar gaba ɗaya sake farfaɗo da harsashinta. Muna buƙatar shugabanni da za su farfaɗo da haɓaka tarbiyyar ‘ya’yanmu, musamman ‘ya’ya mata, da samar da ayyukan yi. Hakan zai rage aikata munanan laifuka a hankali tare da dawo da zaman lafiyar ƙasa.

’Ya’yan da muka kasa tarbiyya a yau ne za su dawo gobe su yi mana ta’addanci. Alamun sun riga sun nuna hakan!

Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, 08168716583.

By ukarofi