Zaɓen ƙananan hukumomi a Kano : NNPP za ta yi wa ‘yan takararta gwajin shan ƙwayoyi 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta sanya  kuɗin fom ɗin takara ga masu neman kujerar shugabancin ƙaramar hukuma kan Naira dubu 500 da Naira dubu 150 ga mai neman kujerar Kansila.

Haka kuma jam’iyyar ta sanya Naira dubu 100 ga masu neman shugabancin ƙaramar hukuma a matsayin kuɗin na gani ina so da kuma Naira dubu 50 ga mai neman Kansila.

Shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Sannan jam’iyyar ta nemi masu shiga takara da su ajiye muƙamansu na siyasa kamar yadda yake ƙunshe a dokokin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC.

Shugaban na NNPP, ya kuma bayyana gamsuwar jam’iyyar da kudin fom ɗin takara na Naira miliyan 10 da miliyan 5 da hukumar KANSIEC ta sanya.

Haka kuma ya ce NNPP ta kama kwamiti da zai binciki takardun karatu na ‘yan takarar da kuma yi musu gwajin shan miyagun ƙwayoyi.

“Za mu sayi katin duba sakamakon jarrabawa na WAEC domin duba ingancin sakamakon jarrabawa na masu neman takara,”  inji shi.

By ukarofi