Abin kunya a Nijeriya (I)

Spread the love

Na kwana biyu ban ce komai ba, hakan kuma ba yana nufin bani da abin cewar ba ne, kawai na koma gefe ne ina kallo da sauraro tare da takaicin abubuwan da suke faruwa a ƙasata Nijeriya, kai ka ce a cikin shirin fim (wasan kwaikwayo) ne ake shirya abinda ke faruwa a ƙasar nan.

Na kira wannan rubutu nawa da suna ‘ABIN KUNYA…’ ne saboda munanan abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan, abubuwan da duk mai tausayi da imani dole ya yi alawadai da halin da ke wakana a ƙasata Nijeriya. Babu ko shakka abin takaici da baƙin ciki ne a ce ƙasa kamar Nijeriya mai tarin arziki da albarkatun ƙasa, amma a ce shugabannin da suke jagorantar ƙasar sun maida ita tamkar hannu jari da zaka saka a kamfani don ka samu riba, kuma ribar a kansu ba a kan talakan ƙasa ba.

Tun a gwamnatin Buhari da ta gabata salon ganawa talaka uƙuba ya sauya, kowa ya gani da idonsa, kuma ya ji a jikinsa ba sai na yi dogon jawabi ba. A ƙasar nan babu wanda bai ɗanɗani ɗacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Buhari ba, sannan nan kuma a yanzu aka ƙara shiga wani mummunan tashin hankalin da yafi na baya a dalilin rashin iya shugabanci.

Tambayar farko da nake so in yi a nan ita ce, shin wai don Allah wane laifi talakawan Nijeriya suka yi wa masu mulki ne, da har idan suna kan mulki ba su ta tasu? A matsayina na marubuci kuma ɗan jarida, nayi iya binciken duk da zan yi a kan dalilin da ya sa talakan Nijeriya ba ya cin ribar mulkin Dimokraɗiyya amma na kasa gano dalilin. Don haka sai nake ganin cewa, da masu mulki a ƙasar nan za su ba talaka haƙƙinsa, to na tabbatar talaka ba zai damu da duk irin satar da za su yi ba.

Na tabbatar da cewa abubuwan da masu mulki suke yi a Nijeriya na rashin hankali da lissafi, da a wata ƙasar ne da tuni an soke mulkin dimokraɗiyya, sai dai sojoji su ci gaba da mulkin ƙasar har abada. Talaka ba kuɗi yafi buƙatar ɗan siyasa ko mai mulki ya ba shi ba, talakawan Nijeriya babu ruwansu da girman gidanka, babbar rigarka ko muƙaminka. Abinda kawai suke buƙata bai wuce su ci su sha a cikin sauƙi ba, kai kuma kayi ta satar kuɗin ƙasa kana tarawa har Mahadi ya bayyana.

Mu kalli yadda ta dalilin rashin iya shugabanci nagari aka kassara harkar noma a Nijeriya (musamman a yankin Arewa). 

Lokacin da tsohuwar gwamnatin Buhari tazo ta rufe iyakokin ƙasa, to daga wannan lokacin harkar noma ta lalace. Duk da cewa daga cikin masana masu kishin ƙasa sun bashi shawarar kar ya yi amma ya yi kunnen-uwar-shegu, ya kulle iyakar ƙasa, sannan ya ɗauko ruɓaɓɓun mutane waɗanda kwakwalwarsu babu tunani mai kyau ya saka su a gurbin (Agricultural), a ƙarshe maimakon kayan abinci ya wadata kuma yayi sauƙi, sai hakan ta faskara. 

Ganin abinci na tsada musamman shinkafa da aka hana shigowa da ita, sai wasu ɓarayin Nijeriya masu wawure kuɗin ƙasa suka riƙa buɗe kamfanonin samar da shinkafa. Da fari mutane sun yi tsammanin hakan zai kawo sauƙi, kuma abinci ya wadata a cikin sauƙi amma sai shinkafa da sauran kayan masarufi suka yi ta hauhawa suna tsada, har sai da ta kai ta kawo shinkafa ta gagari talaka a Nijeriya, garin masara ma sai yayi da gaske yake iya auna. Garin kwaki da ba a damu da shi ba, sai ya zamto shi ake rububi don kar a mutu da yunwa, a nan ma sai garin kwakin ya gagari kundila.

Ana cikin haka sai aka yi canjin kuɗi, talakawa suna kuka suna kokawa amma haka tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aiwatar da wannan tsari. Duk ‘yan ƙasa basu fito sun yi masa bore ba, gwamnoni da ‘yan majalisu, sanatoci da ministoci suna ta wawure kuɗin ƙasa amma duk talaka bai yi bore ba yana ta haƙuri.

Kwatsam! Sai ga wannan gwamnatin ta Bola Tinubu da Kashim Shattima, wadda mutane suke ta fatan ganin an samu sauyi daga gareta, amma a ranar farko da aka rantsar da Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur. Kafin kace haka! Tuni masu gidajen mai suka juya lita suka ƙara kuɗi. A nan ma talakawa suka shiga tasku, duk da suna kokawa amma ba suyi bore ba. Manyan ƙasa suka kama bakunansu suka yi gum, dalili saboda duk wanda ka ke tsammanin zai yi magana makwaɗaici ne, in ma dai an saye shi da kuɗi, ko kuma yana da wata hanyar da yake yin cuwa-cuwa yana satar kuɗin ƙasa.

Haka nan Malaman addinai da yawa sun shiga rigar siyasa, sun zama mabarata ga masu mulki da masu kuɗi da ‘yan siyasa, shi yasa duk abinda ake yi ba su da bakin magana sai dai bayar da haƙuri ga talaka. Haka nan jami’an tsaro sun zama karnukan farauta ga ‘yan siyasa, suna aiki ne don aljihunsu kaɗai ba wai don kare rayuka da dukiyar ƙasa ba. Duk lokacin da ka ji wata doka da oda, to tana wanzuwa ne a kan talaka kawai, amma ba ga waɗanda suka saci kuɗin ƙasa ba.

Misali, mu kalli jami’an tsaron da aka riƙa fitowa dasu a lokacin zanga-zangar lumana da aka shirya a ƙasar nan mai taken (End Bad Goɓernment) da ta yi sanadiyar haifar mana da mummunar tsadar rayuwa, a kowacce jiha an fito da jami’an tsaro masu tarin yawa. Kama daga; Police, DSS, SSS, Sojoji, Ciɓil Defence da sauransu saboda kawai za a yi zanga-zangar lumana. Kafin ranar da aka saka za a yi wannan zanga-zanga, babu irin barazanar da ba a yi wa talakan Nijeriya ba a kan zanga-zangar, amma da yake mutane sun zo iya wuya suka ce ba gudu ba ja da baya sai an yi.

A wajen wannan zanga-zanga an samu wasu jami’an tsaron da suka harbi mutane suka mutu har lahira, haka nan kuma shugaban Nijeriya Tinubu da ya tashi magana, sam bai yi magana a kan dalilin da yasa aka yi zanga-zanga ba, balle har ya magance matsala ɗaya a cikin matsalolin da suka haifar da ita ba.

Babban abin kunya shi ne, sai ma aka ga tsaffin shugabannin Nijeriya da gwamnoni masu riƙe da kujerar mulki, da wasu ‘yan majalisa da sanatoci sun taru sun kaɗa ƙuri’ar amincewa tare da nuna goyon baya ga salon mulkin Tinubu. Iya wannan abin kawai ya zama babban abin kunyar da har abada ba zai gogu ba a tarihin Nijeriya. Daga nan kuma an shirya (National Prayer), har wasu malamai da ‘yan siyasa suka riƙa nuna rashin dacewar hakan. 

Duk mai hankali da tunani idan ya waiwaya baya ya kalli yadda tsohon shugaban Nijeriya Buhari yayi mulki, to zai fahimci cewa Buhari ya ɗaiɗaita ƙasar nan ta yadda idan ba an samu shugaba mai tausayi da tsoron Allah irin Marigayi Alh. Umar Musa ‘Yar’adua ba, to za a ɗauki shekaru da dama kafin Nijeriya ta dawo hayyacinta. Za ku yarda dani idan ku ka kalli salon mulkin Tinubu, shin akwai abinda ya sauya ne na rage raɗaɗi da azaba a tsakanin mulkin Buhari da Tinubu? Nasan za ku ce a’a, dalili kuwa shi ne, tun ba a ci talata da laraba ba ga halin da talakawa suka tsinci kansu a yau a sanadin gurɓataccen mulkin Buhari da Tinubu, da maciya amanar ƙasa daga kowanne ɓangare na wakilan al’ummar wannan ƙasa.

An ce ana so a yi noma don a wadata aasa da abinci, ta yadda ba sai an shigo dashi daga waje ba, kuma mutanen karkara su ne waɗanda suke yin noman nan, amma har yanzu ba a magamce matsalar ‘yan bindiga ba a yankunan karkara da suke kashe mutane, suna koro mutane, suna kashe manoma da ƙonne amfanin gona da tura dabbobinsu su cinye amfanin gonar a lokacin damina.

Zan ci gaba a mako a gaba.

Daga NAFI’U SALISU.

Marubuci/manazarci. Ya rubuto daga Kano Nijeriya. [email protected], [email protected].

By ukarofi