Zaɓen Anambra: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta yi amfani da hedikwatar ta ta yanki da ke Owerri wajen rarraba kayan aiki marasa hatsari na zaɓen gwamnan Jihar Anambra da za a yi.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron bayan wata huɗu da ya kan yi da manyan ‘yan jarida, wanda aka yi a Abuja a ranar Laraba ta wannan makon.

Farfesa Yakubu ya ce an yanke shawarar yin haka ne sakamakon hare-haren da aka kai tare da lalata kayan hukuma a Anambra kwanan nan.

Ya ce kayan aikin zaɓen waɗanda ba su da hatsari su ne za a raba daga ofishin yanki na INEC da ke Owerri zuwa ofisoshin ta na ƙananan hukumomi da ke Anambra.

Ya kuma bayyana jin daɗin ganin cewa hukumar ba ta samu wani sabon hari ba a kan kayayyakin ta tun daga watan Yuni.

Babban Kwamishinan INEC, Farfesa Okechukwu Ibeanu, shi ma ya yi jawabi, inda ya ce yin amfani da ofishin yanki da ke Owerri ya zama tilas domin hukumar ba ta gama wattsakewa sosai ba daga hare-haren da aka kai wa kayayyakin ta a kwanan baya a jihar.

Ibeanu, wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓe da Kayan Aiki (Electoral Operations and Logistics  Committee, EOLC), ya ce sama da kashi 50 cikin ɗari na kayan aiki maras hatsari da aka riga aka tara ne aka lalata a lokacin waɗancan hare-haren.

To amma, a cewar sa, INEC ta tattaro kayayyaki marasa hatsari da ake buƙata, waɗanda su ka haɗa da rumfunan kaɗa ƙuri’a, daga sauran jihohin ƙasar nan.

Ya ce duk da yake an samu cigaba wajen kyawawan hanyoyin mota a Anambra, hukumar ta na kammala shirye-shirye don a rarraba kayan zaɓe da kwale-kwale a yankuna masu yawan rafuka a jihar.

Ya ƙara da cewa hukumar za kuma ta yi amfani da wata manhaja a komfuta wajen sa ido kan aikin rarraba kayan.

Da ya ke bayyana damuwa kan yanayin tsaro a Anambra, Ibeanu ya ce hukumar na yin aiki tare da hukumomin tsaro don tabbatar da an samar da irin tsaron da ake buƙata a zaɓen da za a yi a jihar.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta na buƙatar ma’aikatan wucin gadi kimanin mutum 25,000 da za su gudanar da zaɓen jihar.

Wajen amsa wata tambaya, Ibeanu ya yi watsi da cewa ‘yancin da INEC ta ke da shi a ƙarƙashin kundin tsarin mulki ya sa ta na ɗaukar umarni daga Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) wajen tura sakamakon zaɓe a matsayin abin da ya saɓa wa tsarin mulki.

Ya ce ta hanyar yin aiki da tsarin mulki, hukumar ta na da ƙarfin yin amfani da ikon ta, to amma idan abin ya shafi sanya wani ma’aikacin gwamnatin tarayya ya yi wani aiki to sai shugaban ƙasa ya amince.

Ya ce, “Bari kuma in alaƙanta wannan da shawarar da Majalisar Tarayya ta bayar cewa idan har za a tura sakamakon zaɓe ta intanet, tilas ne INEC ta samu amincewar NCC, ya ce hakan ya yi matuƙar saɓa wa tsarin mulki.

“Ba za mu iya cewa idan INEC za ta tura sakamakon zaɓe sai ta samu amincewar wata hukumar gwamnati ta daban bayan kuma ita INEC ɗin ta na da ikon ta sanya NCC ta cimma nasarar tura sakamakon zaɓen.

“Saboda haka, ni abin da na fahimta kenan da Sashe na Section 162 na Kundin Tsarin Mulki. Na amince da ku ɗari bisa ɗari a kan batun tabbatar da ‘yancin INEC, Sashe na 162 ya kammala komai da ke buƙatar a yi shi.

“Abin da ya rage wa INEC shi ne ta yi amfani da ikon da tsarin mulki ya ba ta.”