Gyara bayan haihuwa

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya: Salam Malama barka da war haka. Ina da tambaya; shin akwai wani tanadi na musamman da mace ya kamata ta yi bayan ta haihu, saboda bayan na yi haihuwar fari sai maigidana ya ke ƙorafi kan na buɗe da yawa kuma Ina bushewa?

Amsa: Akwai abubuwa da dama da mace ya kamata ta mayar da hankali a kansu tun lokacin da take da ciki kama daga abinci da motsa jiki da kulawa da kai da sauransu wanda tun daga lokacin ya kamata a fara tattalin al’amuran da za su biyo baya bayan an haihu. Amma tunda mai tambaya tana tambaya ne bayan haihuwa to bari mu yi bayani.


Bayan mace ta haihu tana buƙatar :-
-A ke shiga ruwan zafi mai tsafta wanda aka saka wa ganyen magarya da gishiri kaɗan na ɗan lokaci.

-Kama ruwa da aka tafasa da Bagaruwa a ƙalla a yi tsarki da shi sau uku a rana.

-Akwai dahuwar kaza ta musamman da ake yi da itatuwa da ganyayyaki don mai jego.

-Shan salala da aka yi da garin hulba akalla sau daya a wuni.

-Shan zuma mai kyau kullum babban cokali a ƙalla sau uku a rana.

-Cin kyakkyawan abinci mai inganci da gina jiki.

-A ci abinci a `ƙoshi ban da zama da yunwa.

-Ban da cin fara da mai.

-A ƙalla nama ko da ba yawa musamman gashi ba soyayye ba ko kuma a yi farfesu. Ya danganta da arziƙin mutum.

-Ya kamata mai jego ta sani tattalin abinci ya fi muhimmanci fiye da tattalin kayan da za a saka ranar suna da kuma abin da za a tara mutane su ci.

-Kula da gashi ko a tsugunna a garwashi da aka tabbatar da tsaftarsa ko ruwan zafi me tsafta (amma bisa yadda likitoci suka shar’anta musamman idan mace ta samu ƙari a yayin haihuwa.

-Yana da kyau a nemi shawarar masana lafiya kan ƙari da mace ke samu a matuncinta yayin haihuwa. Sau tari mace kan haihu a gida kuma ta samu ƙari ba ta tare da ta sani ba. Shi ma irin wannan matsalolin kan janyo rashin jituwa da maigida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *