Daga SHAFIU ALI MAILANTARKI
A ‘yan kwanakin nan mun fuskanci wani abin da ya ɗaure mana kai game da masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. Mun shaidi cewa ita ce masana’anta da a yanayi da zubin gudanarwarta take fama da suka ta fuskoki masu yawan gaske.
Kasantuwar fim abu ne da ake nunawa, wato labari ake bayarwa, wannan ya sa malaman Hausa da Adabin Hausar suke ƙorafin ana ɓatanci ga al’adu da addini a inda aka ce madubi ake yi gare su ana yaɗa su ga al’ummar duniya, duk da cewar iyo ake yi a taƙaitaccen jigo ga ɓata tarbiyya. Ta kai ma suna ta rikiɗewa suna komawa ‘yan rawar disko na bidiyo inda akan samu kalmomi da raye-rayen batsa wanda hakan barazana ne ga tsaftatacciyar al’umma mai rajin kishin Musulunci (wannan ba ra’ayin riƙau ba ne, kishin kai ne irin wanda al’umma ta ginu a kai)
Tare da wannan batu na sama, sun dage a kan suna bunƙasa al’adun Hausawa ne wadda ba za a iya rarrabe su da addini ba ya yiyuwa da daɗin rai. Har sukan soki masu sukarsu, sukan ƙalubalance su da ai zuwa ya kamata su yi a dama da su, kai sai ka ɗauka suna matuƙar sha’awar shigowar wasu a dama da su.
Wani lakcara a fannin Ingilishi kuma marubucin adabi, Hashim Abdallah ya yarda da su a nan, kan haka har ya rubuta wani littafi da harshen Hausa domin masu fasahar samarwa da ƙirƙira ko ƙagar labari, har da marubutan littatafan labarai, tunda labari shi ne ƙashin bayan fim, shi ne dan ba kuma tushe.
Bai tsaya a nan ba, watannin baya ya sake samar da fim na kafar tashar rumbun bidiyoyi (YouTube) da kayan aiki na zamani tare da waɗanda suka san aiki sosai, da kuma sababbin jarumai kuma masu fasaha (saboda manufar fito da sababbi a dama da su), inda suka sakawa shirin suna ‘WUF!’
Asalin kalmar ‘WUF’ tana nufin hanzari ko yin zafin nama ko fakar ido a yi maza a aikata abu, ba ma ya in ana gudun wani/wata/wasu su ankara, musamman wajen yin amfani da wata dama mai ƙurarren taki.
Sai dai WUF a yanzu kuma ta zama wata kalma ce da aka sabunta ta daga Hausawan wannan zamani, akasari matasa maza da mata, ake amfani da ita yayin da wata mace mai shekaru ta auri saurayi mai ƙananun shekaru, ko kuma shi namijin mai tarin shekaru ya auri mace budurwa ‘yar fiririya wacce ba ta wuce sa’ar ‘yarsa ba ko jika ma. Ana cewa wane/wance sun yi wuf da wani ne ga duk auren da ya zamana tsakanin dattijo/dattijuwa mai wata alfarma, kama daga kan tarin dukiya ko matsayi ko sarauta ko mulki ko ɗaukaka ko launin fata na daban da kuma mace ko namijin da ke da ƙarancin shekaru, musamman in yana da ƙarancin dattin aljihu, wato kuɗi.
Amma kuma an zo da abu daban da waɗannan a fim din ‘WUF’. An tsara shi da fassara da Turanci, wato ‘subtitles’ don dalibai da masu nazarin harshe da waɗanda ba sa jin Hausa.
Labari ne na dambarwar soyayyar wani yaro (cima-zaune) ɗan zamani da mahaifiyar abokinsa wadda ba wanda ya san kowa ko waye, amma ko da suka gane ɗin ma, ba su haƙura ba. Abin dubawar, wani irin matsayi ko mataki abokinsa kuma ɗanta ke ɗauka. Shin wace irin soyayyar ma suke yi ne, miye matakin addini ko malamai a kan su?
Shi wannan fim an gina shi ne bisa adabi kan doron addini da al’adar Hausawa, cikin zayyana dalilai da alfanun wannan sabon salo na Wuf da kuma yanda za a bi a kaucewa faɗawa matsalar da ke cikinsa.
Shirin Wuf ya samu aiki daga ƙwararrun ‘yan wasa zuwa kan ma’aikatan da suka shirya tare da ba da umarni, don haka shirin Wuf shiri ne da ya cancanci kallon matasa da dattijai, ko malamai da attajirai, kai har ma da jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati.
Bayan su Hashim Abdallah sun gama rubutawa da tsarawa da tacewa da sauran matasa marubuta, sai ya turawa wani abokinsa sanannen marubucin fina-finai domin a ji daga gare shi ko da tsinkaye ko wasu shawarwari, tare da kalmar, “a sa mana Albarka”
Duk ya ga sakon, bai ba da amsa ko ya yi wata magana a kai ba tsawon watanni. Kuma tun farko sai da ya nemi wannan aboki da ya zo su shirya wa wasu matasa da suke jagoranci fim, musamman a matsayinsa na ɗaya daga cikin uban qungiyar matasan da suke matuqar girmama shi, sai ya ce ayyuka sun yi masa yawa. Ko da aka fara ɗaukar shirin Hashim ya gayyace shi dandali, nan ma dai ya ƙi zuwa kuma ya sake fakewa da wani uzurin.
Bayan watanni huɗu, lokacin da an fitar da fim din WUF daga na ɗaya zuwa na uku, sai ga shi ya haɗe kai da wasu ‘yan fim ɗin da Hashim Abdallah ya fassara da masu ji-ji-da-kai, domin suna kallon kansu su ne masu fim da masana’antar fim gabaɗaya, sun fitar da fasta da sunan fim din WUF iri ɗaya da na su Hashim. Saboda dukkan mai kallon fina-finan Hausa mai alaƙa da shafikan zumunta zuwa yanar Gizo ya san da an yi WUF, domin kuwa banda yawo a yanar gizo ma har da tallar shirin ya yi, jaridar Leadership Hausa da Nigerian Tracker da Mujallar Adabi sun bugo tallar shirin.
Abin mamaki ne aka samu suka turo wani tasharmu yake nuni da cewar wai su a nasu WUF ɗin sun yi amfani ne da ‘f’ guda biyu don haka ba ɗaya ba ne sunan, wanda hakan ba ƙaramin jahiltar ilimin ma’ana ba ne da cin zarafin nahawu ko ƙa’idojin rubutun Hausa ba ne. WUF da WUFF ba su da bambanci a furuci, haka zalika a ma’ana, su ne abubuwan da suka dabaibayi ƙwaƙwalwarsa.
Su Hashim ba su tava nadamar watsa shirin ba domin kuwa da niyya suka saci sunan shirin, kuma duk da haka suka ja hankalinsu da cewa yanzu haka ana cikin yin wannan shirin mai suna WUF fa har an fitar da kashi na 3 a lokacin an ɗauka sunan kawai suka ɗauka, kafin daga bisani a gane jigon labarin ma iri ɗaya ne. Domin nasu WUF din shi ma dai soyayyar ce tsakanin babbar mace da samari (kenan lallai irin namu ne jigon) amma ita bayan ta kashe maigidanta ne a nasu WUF din, jigo ko da yake ita a nasu soyayyar irin ta lalata take yi da samarin.
Lallai, bayan maganar kaucewa addini da al’ada, satar fasaha wata babbar annoba ce ga wasu mashiryan fina-finan Hausa wanda za a daɗe ana kallonsu da shi, kuma wanda zai daɗe yana bibiyar su a duk bajintar da za su yi. Ya zamar musu jiki su juyi shirin India da na Amurka da sauran wasu al’umma har da na ‘yan kudancin ƙasar nan. Ashe ba za su tsaya a nan ba.
Abin takaici ne, in ji Hashim Abdallah, yadda shi wannan aboki nasa fitaccen marubucin bai tsaya a nan ba sai da ya samu wani fitaccen ɗan wasa mai shegen girman kan da yake kamanta wai ganinsa da ganin shugabanni, ya yi batanci ga furodusa Hashim domin yana tunanin sako shi a shirin wanda suke ganin kamar girmaman shi ne. A nan gabar su Hashim suka ce sun tabbatar da Musa a baki Fir’auna a zuci irin na irin waxannan mutane ga rashin girmama sana’arsu a sanadiyyar munanan kalamai na izza da kurari tamkar an tsokani mahaukacin kare, tamkar bai tava zama a aji ba kodayake furodusan shirin WUF na asali, Hashim Abdallah bai yi kasa a gwiwa ba wajen nunawa dan wasan irin tsayuwarsa tsayin dakan da ganar da shi kuskurensa.
Sai dai su ma masharhanta da masana fim ba su ce komai ba game da wannan har yanzu ko don ma tsaftacewa da bunƙasa al’amarin, duk da akwai ƙarancinsu kusa da babu a nan Arewa (saboda rashin ƙasaita ko girmansu a al’amarin, musamman za ka ga ba su iya fitar da bidiyon wani shiri ɗaya ba). Duk da haka, ‘yan kaɗan ɗin ma dai shiru a kan wannan. Sai ka same su ma su ne suke fito da ayyukan barayin fasahar da kansu. Hashim Abdallah ya tabbatar akwai mutum ɗaya da shi ya tura masa bidiyon tallar shirin tun kafin ya fito a watan Fabrairun 2021 ya ce zai juyo gare su, har yau shiru.
An yi wannan rubutun ne don nuna irin baki-biyun masu shirya fina-finai a kan suna son gyara ko shigowar wasu ko sababbi. To, a nan za a ga daga ‘yan fim har zuwa masharhantansa da hukumomi duk ba su cika kai kunyarsu a kan aikinsu ba.
