Zaɓen cike gurbi na Kano: An samu ƙamfar masu kaɗa ƙuri’a yayin da jam’iyyu suka janye

Spread the love

Yayin da aka gudanar da zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin jihar Kano a ƙananan hukumomin Birni da Ungoggo, an samu ƙarancin masu kaɗa kuri’a a mafiya yawan rumfunan zaɓe a yau Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa mafi yawancin rumfunan babu cikowa kamar yadda aka saba, inda aka hango jami’an zaben na gyangyadi a wajen zaben.

An gano cewa a Ƙaramar Hukumar Biri mazaɓun Shahuchi da Sheshe da Jakaka da Zango, ma’aikatan zaɓe na jiran jama’a su fito su kada kuri’ar su tun ‘okacin da a fara kafa kuri’a.

Sannan kuma, wasu akwatunan ma babu wakilan jam’iyyun dake fafatawa a zaɓen, wato agents.

Hakazalika a karamar hukumar Ungoggo, an ruwaito cewa ba a wuce sama da mutum 10 da suka kaɗa kuri’a a yawancin akwatunan zaɓen.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Kwamishinan Zaɓe na jihar Kano, Ambasada Abdu Zango, ya danganta rashin fitowar da yanayi na azumi.

Ya kuma nuna cewa rashin fitowar jama’a ka iya zama sakamakon cewa “ƙaramin zabe” ne da aka yi a ƙananan hukumomi biyu kacal.

Sai dai kuma Abdu Zango ya yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana, sannan ya yabawa jami’an tsaro bisa tsari mai kyau da ya sanya aka yi zaɓen lami lafiya.

Sannan babu jam’iyyar adawa ta NNPP a zaɓen na cike gurbi dake gudana a ƙananan hukumomin, kamar yadda ba a ga pdpdda ADC ba.

Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaida cewa rashin samun ingantaccen shugabanci da yanayin azumi ne ya hana su fitowa.

By Babaji