Zaɓen cike gurbi: PDP ta koka a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Yayin da zaɓukan da za a sake ke gabatowa, jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta zargi ’yan sandan Nijeriya da yunƙurin musgunawa mambobinta a jihar a yayin zaɓen.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta ce, za a sake gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma za a gudanar da zaɓen ne na kujerar ɗan majalisar dattawan Zamfara ta tsakiya da kuma kujeru biyu na majalisar wakilai.

Ofishin yaɗa labarai na Dauda Lawal a ranar Larabar da ta gabata a Gusau ta ce jam’iyyar ta nuna damuwarta game da katsalandan da ake zargin babban Sufeton ’Yan Sandan Jihar Zamfara ya yi.

Jam’iyyar ta kuma ce, gwamnan mai ci ya tsunduma wajen amfani da Sufeto Janar na ’yan sanda wajen aulla maƙarƙashiyar kamawa da kuma tursasa wasu manyan ’yan PDP.

Sanarwar ta qara da cewa, “Muna matuƙar nuna damuwarmu da mugun nufin gwamnan Jihar Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle na siyasantar da ayyukan ’yan sandan Nijeriya ta hanyar amfani da alakarsa da abokan takararsa da Sufeto Janar na ’yan sanda, Usman Alkali Baba.

“’Yan Nijeriya sun san yadda gwamnan jihar ya haɗa baki da Sufeto Janar na ’yan sanda domin yin maguɗin zacen gwamnan da aka kammala a Zamfara.

An tura dakaru na musamman daga Abuja zuwa Gusau da gangan domin kawo cikas wajen bayyana sakamakon ƙarshe. ’Yan sanda sun yi awon gaba da jami’in zave na INEC na ƙaramar hukumar Maradun, inda aka kai shi gidan gwamnati.

“Idan akwai wanda ya buqaci a kama shi da laifin aikata laifukan zaɓe, mun yi imanin cewa gwamna mai barin gado, da mataimakansa, da ’yan sandan gidan gwamnati ya kamata su kasance kan gaba a jerin sunaye.

“A kan wannan batu, muna so mu kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da babban Sufeto Janar na ’yan sanda saboda katsalandan da ya ke yi a siyasar Zamfara.

“Abin mamakinmu, manyan shugabannin jam’iyyar PDP na Zamfara sun samu wasiƙar gayyata daga ofishin babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya kan zargin da ake yi na yin maguɗi a zaɓen 2023.

“Wannan shi ne ƙololuwar rashin sanin makamar aiki da Sufeto Janar na ’yan sanda ke nunawa, kuma mun fusata da shi. Mun yi imanin cewa wannan gayyata wani mataki ne da IGP ya ɗauka na musgunawa tare da tursasa ’yan PDP na Zamfara don hana su shiga zaɓen da za a yi ranar Asabar 15 ga Afrilu.

“Muna ƙara kira ga jama’a da su san halin da ake ciki a Zamfara da kuma yiyuwar amfani da ’yan sanda wajen murƙushe shugabannin jam’iyyarmu, musamman domin kawo cikas ga sake zaɓen ranar Asabar.

Suna da cikakkiyar masaniyar cewa PDP ce za ta lashe kujerar majalisar dattawa ta tsakiya da sauran kujeru biyu na wakilai, don haka suka tsunduma kan ƙoƙarin haifar da rikici.

“Daga cikin shugabannin PDP da Sufeto Janar na ’yan sandan ya gayyata ba bisa ƙa’ida ba, akwai Alhaji Garba Ahmad Yandi, Alhaji Kabiru Ahmadu; Alhaji Yusuf Daha Tsafe; Alhaji Ibrahim Modibbo; Alhaji Zahradeen Ibrahim; Alhaji Musa Malaha; Alhaji Sambo A. Sambo; Hajiya Lubnah Baba Gusau da sauran su.

“Muna kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya kira babban Sufeton ’yan sanda ya ba da umarni. Muna kuma kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da masu sa ido na ƙasa da ƙasa da su sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Jihar Zamfara.