Sojoji sun kashe ’yan bindiga 15 a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar sojoji na ‘Operation Hadarin Daji’ ta Jihar Zamfara ta kashe ’yan bindiga 15 da ke ƙarƙashin shugabancin ƙasurgumin ɗan ta’adda, Dankarami.

Waɗanda aka kashe ɗin sun haɗa da babban kwamandan Dankarami, wanda aka fi sani da ‘Jarfa’.

’Yan ta’addan da suka yi yunƙurin kai hari a yankin Gidan Danjimma da Kirifada da ke cikin ƙaramar hukumar Birnin-magaji a ranar Larabar da ta gabata, sojojin tare da ’yan banga sun yi nasarar fatattakarsu.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, majiya ta shaida wa Blueprint Manhaja cewa ’yan bindigar da yawansu su na gudanar da jana’izar mambobinsu da suka mutu a makabarta a ƙauyen Mai Tsaba da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar.

Wani mazaunin garin Kirifada da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, a ranar Laraba ne ’yan bindigar suka kai wa al’ummar yankin hari, inda nan ta ke aka tattara sojoji, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ’yan ta’addan 15 kenan.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, an jikkata wasu da ba a bayyana adadinsu ba, ciki har da Freezer ɗaya daga cikin waɗanda ake cewa ‘Ba-Sulhu wanda ke cikin manyan mayakan Dankarami.

Sai dai sojoji biyu da ‘yan banga huɗu sun samu raunuka daban-daban a yayin harin.

A wani labarin kuma, hukumomin sojin ƙasar sun ce sojojin sun kuma ceto wasu matafiya da ’yan bindigar suka yi watsi da su bayan wani ƙazamin faɗan da suka yi.

Sojojin da suke sintiri sun samu sahihin rahoto game da ’yan bindigar da suka tare hanyar Danbasa – Bini domin yin garkuwa da matafiya, sannan jami’an tsaro suka garzaya wurin da ‘yan bindigar su ke inda suka yi nasarar kashe ’yan bindigar biyu yayin da wasu suka gudu.

A yayin da ake ci gaba da fatattakar ‘yan bindigar da suka tsere, an samu nasarar ƙwato bindiga qirar AK 47 guda 1 da babur daga hannun ’yan ta’addan.

A nasa martani, kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji a arewa maso yamma, Manjo Janar Godwin Mutkut ya yabawa dakarun tare da yin kira ga al’ummar jihar Zamfara da su cigaba da baiwa jami’an tsaro bayanai kan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *