Zaɓen Edo: Obaseki ya faɗi a ƙaramar hukumarsa

Spread the love

Gwamna Godwin Obaseki ya sha kaye a ƙaramar hukumar sa ta Oredo a hannun jam’iyyar APC kamar yadda hukumar zaɓe ta sanar.

A sakamakon da hukumar zaɓen ta bayyana, ɗan takarar APC ya samu ƙuri’u 30,780 inda ɗan takarar PDP ya samu 24,938, sai ɗan takarar jam’iyyar LP yayi na uku da kuri’a 5,389.

yanzu haka hukumar zaɓen ta cigaba da sanar sauran sakamakon daga sauran ƙananan hukumomin jihar.

By ukarofi