Sanata Ɗandutse ya taya Katsinawa murnar cika shekara 37 da ƙiƙiro Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sanata Muntari Ɗandutse mai wakiltar shiyar Funtua ya taya gwamna Dikko Raɗɗa da al’ummar jihar Katsina murnar cika shekara 37 da ƙirƙiro jihar.

A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun sanatan, ya jinjina wa shugabanin baya da suka jagoranci jihar da irin jagoranci na gari da suka nuna da yasa jihar tayi zarra.

Haka kuma ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da irin gagarumar nasarar da ya suma wajan daƙile ta’addanci a kudancin jihar da yanzu an fara samun zaman lafiya.

Ɗandutse ya jinjina wa gwamnan akan harkan ilimi, musamman ɗaukan malaman makarantar firamare guda 7000 a zangon farko da ƙara ɗaukan wasu malaman gaba da firamare a jihar.

Hakan yace babu shakka wannan mataki da gwamna ya ɗauka akan harkan ilimi zai taimaka gaya wajen rage zaman banza ga matasa da bunƙasa harkar ilimi a jihar.

Sanatan ya taɓo abubuwa da dama da suka haɗa da tallafawa masu ƙananan sana’o’i da ɓullo da tsare tsare na bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Yace a shirye yake da ya bada tashi gudummawa da cikkaken goyon bayan tsare tsare na gwamnatin Dikko Raɗɗa domin ciyar da jihar gaba.

Ɗandutse ya kuma yi albishir ga al’ummar mazaɓar sa na shiyar Funtua cewa romon dimukraɗiyya ma yanzu ya fara antayo masu.

Sai yayi kira ga al’ummar shiyar da su ci gaba da zaman lafiya da hukuri da halin rayuwa da suka sami kansu da cewa in Allah yadda sauƙi na tafe.

By ukarofi