Zaɓen Edo: INEC za ta yi bincike game da zargin sauya sakamako

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike game da zargin sauya sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Edo da a ke gaf da kammala sanar da sakamakonsa.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta tabbatar wa al’umma cewa za ta yi bincike kan zargin.

Kawo yanzu, al’umma su na jiran su ji wani hukunci INEC za ta yi yayin da a ke fatan adalci.

A yanzu haka, hukumar ta fitar da kashi 96.59 na sakamakon zaɓen gwamnan jihar a shafinta na yanar gizo.

By Babaji