Zaɓen Zamfara: Babu wani kame da ‘yan sanda suka yi – AIG Gumel

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, AIG Hassan Mohammed Gumel, ya bayyana kammala zaɓen kujerar ɗan majalisar Jihar Zamfara a Ƙaura Namoda ta Kudu da cewar anyi shi cikin lumana, inda ya ce ba a kama ko mutum ɗaya ba da aikata laifin tada zaune tsaye a lokacin zaɓen.

AIG ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a yau a Shelkwatar rundunar’yan sanda a Gusau.

A cewarsa, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin an gudanar da zaɓen cikin lumana.

A cewarsa, ba a kama wani ko wasu da zargin yunƙuri na kawo cikas ga zaben ba kamar yadda ake raɗe raɗi.

“Ba mu kama wani ko wasu gungun mutane da suka yi yunƙurin karya doka da oda ba a dukkan runfunan zaɓe biyar da aka gudanar da zaɓen kamar yadda ake raɗe raɗi.”

Ya yabawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da suka yi aiki tare ta hanyar tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

“A madadin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, ina so in yaba wa jami’an ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro kan yadda suka kiyaye doka da oda a lokacin zaɓen”. Yace

By ukarofi