Za a sake ba wa al’ummar Katsina damar rajistar tallafin Korona

Daga UMAR GARBA a Katsina

Za a sake ba wa al’ummar Jihar Katsina damar yin rajistar gaggawa ta tatallafin annobar cutar Korona wato ‘Rapid Response Register” a turance musamman ga mutanen da ba su samu damar yi ba tun da farko, inda za a fara rajistar ranar Litanin 7 ga Maris, 2022.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ofishin kula da rajistar mutane marasa ƙarfi na jihar wato SOCU, Marwana Abubakar Darma, ya fitar a madadin babban jami’in shirin a Jihar Katsina, Aliyu Isa Girka.

Sanarwa ta bayyana cewa, mutanen da ke da sha’awar yin rijistar waɗanda kullen annobar cutar COVID-I9 ya shafi kasuwancinsu kuma ba su samu damar yin rajistar ba tun a karon farko, za su iya yin rajistar yanzu.

Sanarwa ta kuma buƙaci jama’a da su guje wa yin rajista sau biyu wanda hakan ya faru a lokacin gudanar da rajistar kashi na biyu kuma ya jaza masu rasa samun damar shiga cikin shirin waɗanda za su amfana da biyan tallafin nan gaba.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, wannan rajista dai za a sake gudanar da ita nan ba da jimawa ba, za ta gudana ne tsawon mako ɗaya kacal, wato daga ranar Litinin, 7 zuwa 13 ga Maris idan Allah Ya kai mu.

Ta kuma buƙaci mazauna garuruwan Jihar Katsina da aka gudanar da shirin a baya, musamman ga waɗanda ba su samu yin rijista ba, da kada su bari a bar su baya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan rajista da za a sake buɗewa, dama ce ga ƙananan hukumomin da ba su samu ikon yi ba a baya sabili da dakatar da hanyoyin sadarwa ta wayoyin salula da aka yi yankunansu, sakamakon matsalar tsaro da aka fuskanta.