Za mu bai wa Gwamna Abba goyon baya don haɓaka ci gaban Jihar Kano – Hon. Ado Tati

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban Jami’ar Siyasa Gangariya na ƙasa, Hon. Ado Tati. Jugo a Jam’iyyar APC ya nuna mutuƙar jin daɗi da farin cikinsa tare da yi wa Allah godiya da ya nuna musu ranar da suka sake haɗuwa a tafiya ɗaya ta siyasa da Gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyarsu ta APC.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida jim kaɗan bayan karɓar Gwamnan jihar Kano Injniya Abba Kabir Yusuf da jagororin  jam’iyyar suka yi a ranar Litinin bayan canza sheƙa da yayi daga NNPP zuwa cikinta. 

Hon Ado Tati ya ƙara da cewa dama can shi tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf akwai  aminintaka ba su taɓa raba gari ba a mu’amala ba, suna  mutunci da shi, mutum ne mai sanin ya kamata da hangen nesa da mutunta mutane.

Ya ce wannan haɗuwa ta siyasa  da aka sake yi tsakaninsu da Gwamnan Kano Injniya Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na amininsa zai ba shi goyon baya da dukkan  gudunmawa da ya kamata wajen bunƙasa cigaban jihar Kano a ƙarƙashin wannan gwannatin.

Hon. Ado Tati Dala shugaban Jami’ar Siyasa Gangariya na ƙasa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf mutumin kirki ne mai ƙwazo da aiki tuƙuru da kishin cigaban al’ummar Kano da yake  yin siyasa bada gaba ba  dawowar sa APC zai daɗa ba shi damar gina cigaban Kano da haɗa kan al’ummarta.

By ukarofi