Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba a Abuja, ya ce sha’awa da jin daɗin ‘yan ƙasar a Mali, Burkina Faso da Nijar su ne fifiko ga shugabannin ƙungiyar ECOWAS, yana mai ba da tabbacin cewa hikima da diflomasiyya za su yi tasiri wajen mayar da ƙasashen cikin ƙungiyar.
Da yake karɓar baƙuncin shugaban ƙasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a ziyarar da ya kai fadar shugaban ƙasa a ɓilla, Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya ce shugabannin ƙasashen uku sun jajirce wajen fitar da shirye-shiryen miƙa mulki tare da bayyana ranakun.
“Dangantakar mu ta mutunta juna za ta ci gaba yayin da muke sake duba halin da ake ciki a ƙasashen uku. Abin da zan iya tabbatarwa shi ne, ba za mu ba gwamnatin da ta saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa haƙuri ba.
“Za mu ci gaba da jagoranci ta misali. Muna da ’yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba waɗanda sojoji suka shafa. Za mu ci gaba da bincika hanyoyin diflomasiyya don kewayawa ba tare da hukunta mutanen da ba su da laifi.
“Za mu ci gaba da ba da izinin zirga-zirga da cinikayya cikin ‘yanci. Ko da yake shirin miƙa mulki ba shi da tabbas, ba za mu hukunta ’yan ƙasa marasa laifi ba; ba su da iko,” inji shi.
Shugaba Tinubu ya shaida wa shugaban na Jamus cewa ƙungiyar yankin za ta bar ƙofa a buɗe domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashen.
“Wannan shi ne abin da ECOWAS za ta tsaya a kai. Duk abin da ke faruwa a cikin ƙasashe, muna kula da jin daɗin ‘yan ƙasa. Ba na son keɓance batutuwa a matsayin shugaban ECOWAS. Za mu bar ƙofa don haɗin gwiwa,” in ji shugaban.
A nasa martanin shugaban na Jamus ya ce sake haɗewar ƙasashen uku zai yi matuƙar tasiri ga tattalin arziki da tsaro a gaɓar tekun yamma.
“Za mu tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu da na yanki. Mun dai yi wata ganawa da Shugaban ƙungiyar ECOWAS. Mun san muhimmancin samun haɗin gwiwar yanki. Mu na cikin Tarayyar Turai.
“Ga Mali, Nijar da Burkina Faso, akwai babban illar tsaro da tattalin arziki na rashin ci gaba tare. Mun fahimci dalilin da ya sa jami’an tsaro na ECOWAS ke dagewa kan harkokin diflomasiyya.
“Ba abu ne mai sauƙi ba amma kuna buƙatar yin amfani da diflomasiyyar ku don ci gaba da kasancewa tare da hukumar da yankin.
Shugaban na Jamus ya ce “Yayin da kuke amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen kawo Mali, Nijar da Burkina Faso don sake tunani kan matsayinsu, ya kamata ku samar da tsare-tsare na gaggawa don haɗin gwiwar tattalin arziki a nan gaba.”