Za mu hukunta duk wanda ya yi maguɗi a zaɓen 2027 — Obi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin hukunta duk wanda ya yi maguɗi a zaɓen 2027, ciki har da jami’an gwamnati da ma’aikatan hukumar zaɓe.

Obi, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron tattaunawa na jam’iyyar NDC a Jihar Nasarawa.

Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da bin dokokin zaɓe tare da tabbatar da cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.

Ya yi alƙawarin magance maguɗin zaɓe tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifin sauya sakamakon zaɓe, ba tare da la’akari da matsayinsa ko tasirinsa a siyasa ba.

Obi ya kuma yi kira da a tsaurara ƙa’idojin karatun da ake buƙata daga masu neman muƙaman zaɓe, yana mai cewa duk wanda ke son tsayawa takara dole ne ya kammala karatun firamare da sakandare.

Ya ce gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci na da muhimmanci wajen ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da cewa shugabanni sun samu nasara bisa zaɓin al’umma.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra, ya sha yin kira da a yi gyare-gyare a tsarin zaɓe.

Sannan ya sha jaddada buƙatar tabbatar da gaskiya da riƙon amana da kuma ƙarfafa hukumomin da ke da alhakin kare dimokuraɗiyyar Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply