Zage damtse nake yi kamar kowane ma’aikacina — Dangote ya bayyana sirrin nasararsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shahararren attajirin Afrika kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa yana kallon kasuwanci ne a matsayin abin sha’awa maimakon aiki, yana mai cewa soyayya ga aiki da kuma ɗa’a su ne manyan sirrin nasararsa a harkokin kasuwanci tsawon shekaru.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi kwanan nan, inda ya ce duk da shekarunsa 69 a duniya, har yanzu yana bin tsayayyen tsarin rayuwa na yau da kullum wanda ke farawa tun da sassafe da motsa jiki kafin ya nufi wurin aiki.

A cewarsa, idan ya ɗauki kasuwanci a matsayin aikin dole kawai, ba zai iya yin irin ƙoƙarin da yake yi a yau ba.

“Ni ina kallon kasuwanci a matsayin abin sha’awa ne, domin da a ce aikin dole ne kawai, da ba zan yi aiki da wannan ƙwazon ba,” inji Dangote.

Da aka tambaye shi irin yadda yake aiki tuƙuru, sai ya ce yakan kwanta da dare wajen ƙarfe 11 ko 12, sannan ya tashi da misalin ƙarfe 5 na safe domin zuwa motsa jiki.

“Da misalin ƙarfe 7:30 ko 8 na safe na gama motsa jiki, sannan na nufi ofis, inda nake aiki kamar yadda kowanne ma’aikaci yake yi, duk da cewa yanzu ina da shekaru 69,” inji shi.

Dangote ya kuma bayyana cewa ƙudurinsa na bunƙasa masana’antu a Nijeriya ne ya sa ya sayar da wasu manyan kadarorinsa na alfarma da ke ƙasashen Amurka da Birtaniya domin mayar da hankali gaba ɗaya kan kasuwancinsa a Nijeriya.

Ya ce dabarunsa na kasuwanci sun fi karkata ne wajen samar da kayayyakin da al’ummar Afrika ke amfani da su a kullum maimakon ci gaba da dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje.

A cewarsa, kamfanoninsa suna zuba jari ne a fannoni irin su siminti, sukari da fulawa ta hanyar tsarin da ya kira “backward integration”, wato samar da kayayyakin cikin gida maimakon dogaro da shigo da su daga waje.

Attajirin ɗan kasuwar ya ƙara da cewa duk wani matakin kasuwanci da yake ɗauka yana dogara ne da tsare-tsare na dogon lokaci da kuma hangen nesa, duk da cewa ya amince cewa wasu fannoni kamar masana’antar yadi da sarrafa fulawa sun fuskanci ƙalubale sakamakon matsalar canjin kuɗaɗen waje.

Dangote ya jaddada cewa ɗa’a, jajircewa da hangen nesa na dogon lokaci su ne ginshiƙan samun nasara a harkokin kasuwanci.

Bayan fitowar hirar, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yaba da yadda Dangote ke kula da lafiyarsa ta hanyar zuwa motsa jiki duk da shekarunsa.

Wasu kuma sun ce hirar ta nuna muhimmancin aiki tukuru, ƙwazo da kuma mayar da sana’a abin sha’awa domin samun ci gaba a rayuwa.

By ukarofi