Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta Nijeriya (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Nijeriya ta ƙaru zuwa kashi 15.69 cikin ɗari a watan Afrilun 2026, idan aka kwatanta da kashi 15.38 cikin ɗari da aka samu a watan Maris.
Rahoton da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ya nuna cewa ƙarin tsadar kayan abinci, sufuri, masauki, lafiya da sauran kayayyaki ne suka janyo hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka a faɗin ƙasar.
A cikin rahoton ‘Consumer Price Indeɗ’ da hukumar ta wallafa, NBS ta ce hauhawar farashin ta watan Afrilu ya nuna ƙarin kaso 0.31 cikin ɗari idan aka kwatanta da watan Maris na shekarar 2026.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ma’aunin farashin kayayyaki na CPI ya ƙaru zuwa maki 138.3 a watan Afrilu, daga maki 135.4 da aka samu a watan Maris.
Sai dai duk da ƙarin da aka samu a matakin shekara-shekara, rahoton ya nuna cewa saurin tashin farashi na wata-wata ya ragu. A tsarin wata zuwa wata, hauhawar farashin ta tsaya ne a kashi 2.13 cikin ɗari, ƙasa da kashi 4.18 cikin ɗari da aka samu a watan Maris.
NBS ta bayyana cewa wannan na nufin yadda farashin kayayyaki ke ƙaruwa a watan Afrilu ya yi ƙasa idan aka kwatanta da yadda ya ƙaru a watan Maris.
Rahoton ya nuna cewa abinci da abubuwan sha marasa giya su ne suka fi taka rawa wajen haifar da hauhawar farashin, inda suka bayar da kaso 6.40 cikin ɗari na jimillar hauhawar farashin.
Bangaren gidajen abinci da masauki ya bayar da kaso 3.56 cikin ɗari, yayin da sufuri ya bayar da kaso 1.70 cikin ɗari. Haka kuma ɓangaren lafiya ya bayar da kaso 1.21 cikin ɗari, sai gidaje, ruwa, wutar lantarki da makamashi da suka bayar da kaso 0.77 cikin ɗari.
Sauran ɓangarorin da suka taimaka wajen tashin farashin sun haɗa da kayan kwalliya da hidimomi daban-daban, ilimi, tufafi da takalma, da kuma sadarwa.
A ɓangaren abinci kuwa, NBS ta ce hauhawar farashin abinci ya kai kashi 16.06 cikin ɗari a watan Afrilu, idan aka kwatanta da kashi 24.68 cikin ɗari da aka samu a watan Afrilun bara.
Hukumar ta danganta tashin farashin abinci da ƙarin kuɗin hatsi da kayan masarufi kamar gero, garin doya, citta, naman sa, garin rogo, doya, barkono, kifi busasshe, wake, dankalin Irish, tumatir, alkama, waken soya, dawa da ayaba.
A matakin jihohi kuwa, Jihar Sakkwato ce ta fi fama da hauhawar farashi da kashi 25.74 cikin ɗari, sai Bauchi da kashi 22.52 cikin ɗari, yayin da Zamfara ta zo ta uku da kashi 22.03 cikin ɗari.
A gefe guda kuma, Edo ce ta fi samun sauƙin hauhawar farashi da kashi 5.91 cikin ɗari, sai Borno da Jigawa.
Rahoton ya kuma nuna cewa Jihohin Enugu, Kwara da Adamawa ne suka fi fama da tashin farashin abinci, yayin da Borno, Jigawa da Taraba suka fi samun sauƙi a wannan ɓangare.
NBS ta yi gargaɗin cewa ya kamata a yi taka-tsantsan wajen kwatanta alƙaluman jihohi saboda bambancin tsarin kashe kuɗi da yanayin rayuwa tsakanin jihohin Nijeriya.
Haka kuma, ƙungiyar Dillalan Kasuwannin Kuɗi ta Nijeriya ta yi hasashen cewa hauhawar farashin za ta iya kaiwa kashi 16.42 cikin ɗari a watan Afrilu, sakamakon tsadar abinci da makamashi da kuma hauhawar farashin kayayyaki a kasuwannin duniya. Sai dai alƙaluman da NBS ta fitar sun nuna cewa hauhawar ta tsaya ƙasa da hasashen da aka yi.
