Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta gina tsarin gudanar da haraji mai tsare gaskiya, tare da mayar da hankali kan buƙatun ’yan ƙasa, a wani ɓangare na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja yayin ƙaddamar da gidan yana na hukumar da kuma cibiyar karɓar kiran waya kyauta ta ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji.
Ministan ya bayyana ƙaddamar da sababbin dandalan a matsayin wani babban mataki na ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin haraji a Nijeriya. Ya ce, “Wannan wani babban mataki ne wajen ƙarfafa amincewar jama’a da inganta samun damar amfani da ayyuka tare da tabbatar da adalci a tsarin gudanar da haraji na Nijeriya.
“Ingantacciyar hanyar sadarwa da haɗin kan jama’a suna da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar irin waɗannan sauye-sauyen tattalin arzikin.”
A cewar Idris, gwamnatin Shugaba Tinubu tana ci gaba da aiwatar da muhimman sauye-sauye domin ƙarfafa tara kuɗaɗen shiga, tabbatar da ɗorewar tattalin arziki da kuma bunƙasa cigaban ƙasa.
Ya ce, “ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da jajircewa wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi, mai ɗorewa kuma mai wadata ta hanyar muhimman sauye-sauye masu ma’ana.”
Ministan ya ce, haraji yana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar samar wa gwamnati kuɗaɗen da ake amfani da su wajen bunƙasa ababen more rayuwa da kiwon lafiya da ilimi da sufuri da tsaro.
Sai dai ya jaddada cewa tsarin gudanar da haraji ba zai yi nasara ta hanyar tilastawa kawai ba, sai an gina shi bisa amincewar jama’a da gaskiya da adalci.
Ya ce, “Tsarin gudanar da haraji ba zai yi nasara ta hanyar tilastawa kawai ba. Dole ne ya samu goyon bayan jama’a tare da kasancewa bisa gaskiya da adalci da kuma ingantacciyar sadarwa.”
Idris ya bayyana cewa ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji wata muhimmiyar gada ce tsakanin masu biyan haraji da hukumomin haraji, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na samun damar gabatar da ƙorafe-ƙorafe cikin gaskiya da ƙwarewa.
Ya yaba da ƙaddamar da cibiyar karɓar kiran waya kyauta da kuma shafin gidan yana na hukumar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa sadarwa da samun bayanai da ayyuka.
“ƙaddamar da cibiyar karɓar kiran waya kyauta tana nuna aniyar gwamnati ta kawar da matsalolin sadarwa tare da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya za su iya neman bayanai da gabatar da tambayoyi da kuma warware ƙorafe-ƙorafen su ba tare da wata wahala ko ƙarin kuɗi ba.”
Ministan ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a kan haraji domin ƙarfafa biyan haraji da kuma inganta kishin ƙasa.
“Wayar da kai kan haraji ba wai don tara kuɗaɗen shiga kawai ba ne, don gina al’adar haɗin kan ƙasa da ɗaukar alhaki tare ne,” inji shi.
Ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya da rashin ingantacciyar sadarwa suna hana sauye-sauyen gwamnati samun karɓuwa tare da haifar da rashin amincewa daga jama’a.
Ya ce: “Yaɗa labaran ƙarya da rashin isasshiyar sadarwa sukan haifar da rashin amincewa da kuma ƙin karɓar sauye-sauye. Wannan yana nuna muhimmancin amfani da kafafen yaɗa labarai yadda ya kamata da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a.”
Ministan ya sake tabbatar da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da tsare aiki tare da Ofishin Taɗ Ombud da sauran hukumomin da abin ya shafa domin wayar da kan jama’a kan sauye-sauyen haraji da haƙƙin masu biyan haraji da hanyoyin warware ƙorafe-ƙorafe.
Ya ƙara da cewa, ingantacciyar sadarwa za ta taimaka wajen fahimtar rawar da haraji ke takawa wajen tallafa wa Ajandar Sabunta Fata da ci gaban ƙasa.
Ministan ya taya Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji murnar ƙaddamar da sabbin dandalan tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai domin gina tsarin haraji mai gaskiya da inganci wanda zai amsa buƙatun ’yan Nijeriya.
Taron ya samu halartar Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele; Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack; Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji, John C. Nwabueze; da sauran manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki.
