Zama alƙalin-alƙalai ne babban burina – Barista Fatima Musa

“Mu na buƙatar yawaitar lauyoyi mata don kare ‘yan uwanmu mata”

Daga ABUBAKAR  M. TAHIR

Barista Fatima Musa matashiya ce wanda ta ke lauya mai shekaru talatin, yanzu haka tana digirinta na biyu a fannin na lauya. A cikin tattaunawarta da Wakilin Blueprint Manhaja, Abubakar M. Tahir, ta kawo muhimman batutuwa da suka shafi ƙarancin mata lauyoyi da ma shawarwari ga mata musamman wajen neman ilimi koda suna gidajen aurensu ne. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.
BARRISTER FATIMA: Assalamu alaikum wa rahmatullah. Sunana Fatima, an haifeni a garin Kano, a ranar 14 ga watan Oktoba, 1992, wanda yanzu haka ina da shekaru talatin. Na yi makarantar ‘Addy nursery da Primary’ a shekarar 1998 zuwa 2003, daga nan na yi BUK ‘staff secondary school’, daga shekarar 2003 zuwa 2009, sai na samu ‘admission’ a Bayero University Kano, a tsangayar koyon aikin lauya, inda na karanci lauya daga 2009 zuwa 2014. Na samu shedar zama lauya wato LLB, a shekarar na samu miji, na kuma yi aure. ina auren lauya ɗan’uwana.
Haka kuma a shekarar na samu ‘admission’ a ‘Law school’ wato 2014, a Abuja, inda na gama 2015, na samu shedar BL wato na zama cikakkiyar lauya, haka kuma a wannan shekarar na samu damar tafiya bautar ƙasa, na gama 2016, inda a 2018 na samu ‘admission’ a Bayero inda zan yi ‘Masters’ wanda ake kira da LLF. Da yake yana da vata lokaci, amma insha Allah mun kusa gamawa. Kuma duk da ina karatu, cikin hikimar Allah a shekarar 2020 na samu aiki da FCT ‘judiciary’ inda yanzu haka ni ‘rijistar’ ce ta koto. kuma babban burina shine, na zama ‘justice’ ta ‘suprime court’ wato alqali a ɓangaren kotun ƙoli, haka kuma na ga ilimin ‘ya’ya mata ya inganta.

Waɗanne nasarori za a ce kin samu kawo wa yanzu?
Alhamdulillah. Nasarori sai dai mu gode wa mai dukka. Nasara babba, samun damar na yi karatu cikin ƙanƙanin lokaci, na zama lauya, na kuma yi aure, ga shi Allah ya azurtani da yara uku, ga kuma aiki da na ke, sannan kuma ina cigaba da karatuna na digiri na biyu a fanninin da na ke, kuma kowanne na tafiya yadda ya kamata, ina iya ƙoƙarina wajen sauke nauyin kowanne ɓangare daga ciki, iyali, wurin aikina da ma ci gaba da karatuna.

Ko akwai ƙalubale da za a ce kin samu wajen tauna taura biyu a lokaci guda, wato aure da karatu?
To maganar gaskiya ba zan ce na samu wasu ƙalubalai ba a lokacin da na ke karatu ba, kuma tun tasowa ta dama karatun mu ke, haka kuma na yi aure shi ma lokacin babu wata matsala da na samu. maganar a nan ita ce, aure bai hana karatu, amma sai mutum ya samu goyon baya, musamman maigida wato miji, indan aka samu miji mai fahimta, babu wata damuwa, haka kuma ga shi ina da yara, amma duk a hakan ake yi babu wata matsala da za a ce.

Da ya ke ana fama da ƙarancin mata ‘yan Arewa a ɓangaren da ki ke wato lauyoyi. Me ki ke ganin yake yanyo hakan?
To maganar gaskiya shi ne, ana fama da ƙarancin ilimin lauyoyi musamman mata, kuma ‘yan Arewa, don ko a lokacin mu na ‘Law School’ za ka ga babu ‘yan Arewa mata da yawa. Kuma shi wannan ɓangare ilimi ne mai matuƙar amfani, musamman za kaga ana fama da cin zarafin ‘ya’ya mata ta hanyar yi mu su fyaɗe, cin zarafi a gidajen aure, ka ga namiji yana dukan matarsa, haka kuma akwai take haƙƙi da yawa da ake yiwa mata, wanda kuma amfanin mata lauyoyi zai yi amfani kenan, domin za su fi sa ƙaimi wurin kwato wa ‘yan’uwansu haƙƙinsu. Lauya na taka rawa a rayuwar al’umma fiye da yadda suke ɗauka, domin duk inda ake rayuwa babu doka ‘law less society’ za ka ga kamar ana rayuwar dabbobi ne. Kuma shi lauya matuƙar ana rayuwa dole a buƙace shi. Domin mutum idan yana da koke zai ɗauke shi ne ya kai wurin lauyoyi, don su tsaya kai da fata wajen ganin sun lalubo masa haƙƙinsa a duk inda yake. To kaga karantar wannan fage za mu iya cewa ya zama dole a al’umma. Yawancin cin zarafin mata da ake ba sa iya furta wa, sukan yi shiru ne sakamakon ƙarancin waɗanda za su kai ƙara. Idan ya zama akwai yawaitar masu wannan karatun, to maganar gaskiya za a ce yawaitar laifuka zai ragu. Don haka ya kamata ‘yan Arewa musamman mata su zage dantse su shigo wannan karatu domin kwato wa al’ummarmu haƙƙinsu.

Wani kira ki ke da shi ga ‘yan’uwanki mata masu sha’awar karantar wannnan fanni?
To, a gaskiya ina kira ga ‘yan’uwana mata, su sani ɓangaren lauya yana da buƙatar mutum ya jajirce, idan har mutum ya dage zai kai ga samun nasara, haka kuma dole ne mutum ya dage da addu’a, domin ita ce magani, ita ce ta ke kai mutum ga samun nasarori a rayuwarsa, sannan kuma da addu’ar iyaye ita ma tana ta ka muhimmiyar rawa wajen samar wa mutum nasara. Ba ni manta wa, tun mu na ƙanana, za ka ga iyayenmu na yawan ce ma na,  mu yi addu’a idan za mu shiga jarrabawa, wannan yana taimaka ma na sosai ya ma zame ma na jiki, to maganar gaskiya a dage a kuma yi addu’a, za a kai ga cinma nasara. Mu sani cewa, shi ilimi wani jigo ne wanda babu uzuri ko a addinance kan neman ilimi musamman kuma ilimin ‘ya’ya mata, wanda idan ka ilimintar da mace ka ilimintar da al’umma ne, tunda mace ita ce ta ke bada tarbiyya ga ‘ya’yanta, idan kuwa suka gyaru, al’umma za ta gyaru.

Wanne kira kike da shi ga iyayenmu kan barin ‘ya’yansu su yi ilimi? 
To, maganar gaskiya kiran da na ke da shi ga iyayen shi ne; mu daure mu rinƙa barin yaranmu mata suna yin ilimi, wannan ta sa za ka ga yawanci rashin tarbiyya da matasanmu suke fama da ita tana samo asali ne daga halin ƙarancin tarbiyya daga iyayenmu mata. ilimi haske ne, yana fitar da mutum daga duhun jahilci, musammman iyayen da ke ɗorawa yaransu talla, za kaga ba ta da wani amfani, idan mu ka daure mu ka yi ilimi hakan zai fitar da mu daga ƙangin da mu ke ciki, ko a kasuwanci akwai banbanci da me ilimi da jahila, wannan ta sa a kullum mu ke kira ga iyaye kan barin yaransu su yi ilimi domin ciyar da al’umma gaba.

Wani kira kike da shi ga matasa musamman ta ɓangaren rashin aikin yi?
To alhamdu lillah, a gaskiya ana fama da rashin aikin yi. Za kaga a yanzu masu digiri, MSC suna zaune babu abin yi, wannan ta sa dole matasanmu su san mene ne goben su za ta yi, mu rinƙa ƙoƙari wajen koyon sana’o’in hannu, mu kuma dage wajen muhinmantar da sana’ar, haka kuma mu ci gaba da neman aiki har Allah ya sa akai ga nasara. Ga sana’o’i nan ga mata kamar girke-girke, ɗinki, siyar da kayan shadda da dai sauransu. Mu rinƙa yi duk sana’a idan dai babu hamarci a cikinta, matasanmu su daure su koye ta.

Wani kira ki ke da shi ga hukumomi wajen tallafa wa ɓangaren ilimi?
To, a gaskiya kiran da na ke da shi ga hukumomi shi ne; su taimaka wajen tallafa wa ɓangaren ilimi, haka wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin neman ilimi. yawanci za kaga ana fama da ƙarancin malamai da kayan aiki, to dole ne gwamnati ta wadata makarantu da kayan aiki domin samar da ilimi mai inganci.

Mun gode.
Ni ma na gode.