Zaman NEC: ‘Yan sanda sun karɓe iko a Sakatariyar PDP da umartar mambobin Kwamitin Amitattu su bar farfajiyarta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar ranar Litinin ne jami’an ƴan sanda suka karɓe iko da Wadata Plaza, wato Hedikwatar babbar jam’iyyar adawa (PDP) dake Abuja, a sakamakon fargabar rikicin zaman Kwamitin Majalisar Zartarwar jam’iyyar (NEC), wanda ake sa ran gudanarwa a yau.

Ƴan sandan sun hana mambobin kwamitin amitattun (BoT) jam’iyyar ciki har da Maina Chiroma shiga farfajiyar Sakatariyar.

Tsohon Sakataren jam’iyyar, Umar Tsauri ya shaida wa manema labarai cewa, ƴan sanda sun kafa musu hujja da cewa an ba su umarnin hana mambobin Bot shiga ne daga mataki na sama.

Daga bisani an ga yadda mambobin na Bot suka fice daga sakatariyar.

Wani jami’in jam’iyyar ya bayyana cewa, an baza jami’an ne da nufin hana yin zaman NEC wanda aka faɗaɗa zuwa babban zama na jiga-jigan jam’iyyar.

Duk da ce an bar wasu yan jam’iyyar sun shiga cikin sakatariyar da fari, daga baya an kore su, sannan kuma aka umarci ƴan jarida su bar yankin baki ɗaya.

By Babaji