Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kammala shirye-shiryen dawo da ɗaliban ta da ke karatu a jami’ar ƙasar Cyprus a halin yanzu, domin ba su damar kammala karatun digiri a jami’o’in Nijeriya.
Kwamishinan Ilimi, Kimiya da Fasaha na Jihar Zamfara, Alhaji Wadatau Madawaki ya bayyana haka lokacin da yake karɓar masu ruwa da tsaki na ƙungiyar ɗaliban Jihar Zamfara (FAZAMS) da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa jiya Alhamis.
A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a dawo da ɗaliban kafin ƙarshen wannan shekara.
Ya ƙara da cewa, ma’aikatarsa tare da haɗin gwiwar hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha sun yi kyakkyawan tsari, don tabbatar da cewa ɗaliban ƙasar Cyprus za su shiga jami’o’in bisa la’akari da kwasa-kwasai da matakan karatu, domin su kammala kammala karatunsu cikin nasara a Nijeriya.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a baya-bayan nan rahotanni sun nuna cewa, ɗaliban Jihar Zamfara da ke karatu a ɗaya daga cikin jami’o’in ƙasa da ƙasa da ke ƙasar Cyprus sun shiga wani mummunan yanayi daga mahukuntan jami’ar, saboda rashin biyan su kuɗaɗen makaranta.
A cewarsa, an tura wani kwamitin mutane uku a ƙarƙashin jagorancinsa zuwa jami’ar Cyprus International Uniɓersity, amma sai aka gano cewa ɗaliban ba sa samun cikkakkiyar kulawa daga mahukuntan jami’ar, saboda gwamnatin da ta gabata ta tura su ne ba tare da wani ingantaccen yarjejeniya ba, yanayin da a cewarsa ya jefa ɗaliban cikin tsananin rashin tabbas da wahala.
Kwamishinan ya yi kira ga ƙungiyar FAZAMS da ta ba wa gwamnatin jihar haɗin kai a kodayaushe, domin gudanar da ayyukan jin daɗinsu.
A yayin da ya ke jawabi tun da farko, shugaban masu ruwa da tsaki na ƙungiyar, Kwamared Umar Mahmud, ya ce, sun je ofishin kwamishinan ne domin neman goyon bayan gwamnatin jihar ta hanyar samar da tallafin karatu ga ɗalibai, samar da sakatariyar ƙungiyar ta dindindin, samar da asusun tallafi ga dɗalibai da kuma samar masu da mota mai cin mutum 18, don ci gaban ƙungiyar.
