Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba ya jin wani ƙalubale wajen kwana a otel mafi muni, duk da ɗimbin arzikinsa, yana mai jaddada muhimmancin sauƙin kai da rayuwa ba tare da nuna isa ba, ko da mutum yana da dukiya ko matsayi a cikin al’umma.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taro mai taken Vision 2030, inda ya kuma amince da gayyatar da wani fitaccen mai shirya abubuwan nishaɗi da yaɗa shirye-shirye a intanet, Adebayo Ridwan, wanda aka fi sani da Bae U Barbie, ya yi masa domin ya fito a shirin sa na YouTube mai suna Curiosity Made Me Ask.
Attajirin ya ce, ya yi imani da rayuwa cikin sauƙi, ba tare da barin dukiya ko nasarorin da mutum ya samu su sa ya ɗauki kansa a matsayin wanda ya fi sauran mutane ba. Ya ce, “Ina kuma son in nuna wa mutane cewa a rayuwa, ya kamata mutum ya kasance mai sauƙin kai gwargwadon iko, domin kowa na iya zama wani abu a rayuwa.”
Da yake ƙarin bayani kan yadda yake kallon rayuwa, Dangote ya ce duk da kasancewarsa hamshaƙin attajiri kuma ɗan kasuwa mai manyan masana’antu, zai iya rayuwa a wurare masu sauƙin yanayi ba tare da damuwa ba. Ya ce, “A yau, ko da ka kai ni duk inda kake so, har ma da otel mafi muni, zan iya kwana a wurin, in yi wanka, kuma in rayu ba tare da wata matsala ba.”
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka, rayuwa tana buƙatar sauƙin kai. Ya kamata mutum ya guji ɗaukar kansa a matsayin wanda ya fi kowa ko kuma ya ɗaga kansa sama da sauran mutane.”
Domin ƙarfafa hujjojinsa, Dangote ya ba da labarin abotarsa da Firaministan Habasha, inda ya bayyana cewa shugaban ya shafe shekaru takwas a kan muƙaminsa ba tare da amfani da direba ba. Ya ce a lokacin da ya kai ziyara ƙasar domin ƙaddamar da wata masana’antar samar da takin zamani, ya tambayi firaministan dalilin da ya sa ba ya amfani da direba. A cewar Dangote, firaministan ya bayyana masa cewa matarsa ce ke tuƙa masa mota.
Jawaban Dangote sun zo ne bayan Bae U Barbie ya gayyace shi domin ya fito a shirinsa na Curiosity Made Me Ask, yana mai cewa ya kamata a bai wa matasan Nijeriya damar jin labaran gogewa da ƙwarewa kai tsaye daga manyan ’yan kasuwa da suka yi fice.
Bae U ya bayyana cewa yawancin hirarrakin da aka taɓa yi da Dangote a baya sun fito ne a kafafen yaɗa labarai da matasa ba sa yawan kallo, duk da cewa suna da sha’awar sanin harkokin kasuwancinsa da shirye-shiryen sayar da hannun jari na kamfaninsa ga jama’a a karon farko.
Da yake mayar da martani kan gayyatar, Dangote ya ce matasa su ne makomar al’umma, don haka ya zama wajibi ga tsofaffin al’umma su zauna da su, su kuma raba musu gogewa da darussan da suka koya a rayuwa. Ya ce, “A gaskiya, matasan da kuke gani a yau su ne makomar da muke da ita. Mu na zamaninmu, gaskiya ba mu yi wa Nijeriya da Afirka abin da ya kamata ba. Wannan ita ce gaskiya.” Ya ƙara da cewa, “Saboda haka, muna buƙatar mu zauna da wasu daga cikinku, mu tattauna tare da ku, mu kuma raba muku abubuwan da muka koya a rayuwarmu.”
Dangote ya ce matasa suna da muhimmanci a gare shi, musamman ganin yadda suke ci gaba da nuna masa goyon baya da girmamawa. Attajirin ya kuma yi bayanin dalilin da ya sa yake saurin amincewa idan mutane suka nemi ɗaukar hoto tare da shi, duk da matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwa a duniya.
Ya tuna wani lamari da ya faru a lokacin ƙuruciyarsa, lokacin da shi da kakansa marigayi suka haɗu da wasu fitattun mutane a birnin Washington na Amurka, suka kuma nemi ɗaukar hotuna tare da su. Dangote ya ce wannan ƙwarewa da ya samu tun yana matashi ta yi tasiri a kansa, har ta sa yake ganin ya dace ya amince da buƙatar duk wanda ya zo gare shi domin su ɗauki hoto tare.
