Zan iya taimakon gwamnatin Tinubu wajen shawo matsalolin tattalin arziki, amma ba zan yi ba – Sarki Sunusi

Daga USMAN KAROFI

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce ba zai bayar da shawara ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yadda za a magance matsalolin tattalin arzikin ƙasar ba.

Sanusi ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin gabatar da jawabinsa a taron tunawa da marigayi Cif Gani Fawehinmi karo na 21, da aka gudanar a Legas. Yayin da yake jagorantar taron, Sanusi ya ce ya fara taimaka wa gwamnati a baya amma yanzu ya yanke shawarar daina yin hakan.

A cewarsa: “Zan iya bayar da wasu mahimman bayanai kan abin da muke fuskanta da yadda za a iya gujewa hakan. Amma ba zan yi ba.

Na yanke shawarar daina magana kan tattalin arziki ko gyare-gyare saboda idan na yi, zai taimaka wa wannan gwamnati. Amma ba na son taimaka wa wannan gwamnati. Duk da cewa abokaina ne, idan ba su yi kamar abokai ba, ni ma ba zan yi kamar aboki ba.”

Ya ci gaba da cewa: “Ba su da mutane masu cancanta da za su iya fito da bayanai kan abin da suke yi. Ba zan taimaka ba. Na fara da taimaka wa gwamnati, amma yanzu na daina. Bari su fito su yi wa ‘yan Najeriya bayani kan dalilin da ya sa suke bin waɗannan manufofin.”

Sanusi ya kuma bayyana cewa abubuwan da ake fuskanta yanzu sun kasance sakamakon shekarun da aka yi ana tafiyar da tattalin arzikin ƙasar ba tare da ingantattun tsare-tsare ba. Sai dai ya ce ba komai ake yi daidai ba, kuma idan lokacin ya yi, zai faɗi albarkacin bakinsa kan tattalin arziki.

Har ila yau, ya yi kira ga lauyoyi da su yi koyi da halaye nagari na marigayi Gani Fawehinmi, wanda ya ce ya zama cikakken misali na kyawawan ɗabi’u ’u da ake buƙatar gani a cikin aikin lauya.