Zanga-zanga da tasirinta kan tattalin arziƙi

Spread the love

Daga IBRAHIM ABUBAKAR LAJADA

A sakamakon yadda wani ɓangare na ‘yan Nijeriya ke ta zuguguta batun fita zanga-zanga a dukkan faɗin ƙasar nan, akwai wasu abubuwa da suke ɗaukar hankalin masana game da tasirin da hakan zai yi ga tattalin arziƙin ƙasa. Duk da kasancewar babu wanda yake musu kan muhimmancin zanga-zangar lumana a matsayin hanyar bayyana rashin jin daɗin yadda gwamnati ke gudanar da wasu al’amura, amma yana da matuƙar muhimmanci mu fahimci illar da hakan zai haifar ga cigaban tattalin arziƙi da ɓarnatar da dukiya ko haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci da zaman lafiya. Lallai ne mun fahimci cewa ‘yan Nijeriya suna da haƙƙi da ‘yancin shirya zanga-zangar lumana a ƙarƙashin tsarin dimukraɗiyya, sai dai kuma idan har wannan zanga-zangar ta ɗauki lokaci ko aka samu shigar ɓatagari a ciki, babu shakka za a samu ƙalubale sosai ta fuskar kasuwanci da cinikayya. Na san wasu daga cikin masu yunƙurin shirya wannan zanga-zangar a wasu jihohin ƙasar nan, kuma a shirye nake na taimaka wa gwamnati wajen shiga tsakani don a sasanta ya zama an dakatar da wannan zanga-zanga.

Yadda zanga-zanga ke tasiri wajen gurgunta harkokin tattalin arziƙi

Kowacce irin zanga-zanga da ake yi da ta shafi wasu muhimman batutuwa na cigaban ƙasa tana da tasiri ga harkokin tattalin arziƙi. Kamar misalin:

Katsewar harkokin kasuwanci: a lokacin da ake zanga-zanga ana fuskantar katsewar harkokin kasuwanci, inda ake rufe kasuwanni da shaguna na tsawon wasu awoyi. Wannan yana janyo da asara mai yawa, da durƙusar da saye da sayarwa, da masu sana’anta kayan da ake sarrafawa, musamman ma ƙanana da matsakaitan sana’o’i, waɗanda su ne suke juya tattalin arziƙin da ke shiga hannun talaka.

Katsewar safarar kayan da aka sana’anta: Zanga-zanga na haifar da katsewar jigilar kayan da kamfanoni da masu masana’antu suka sarrafa, don kai wa ga kasuwanni a gari-gari, saboda aana datse hanyoyi a hana zirga-zirga. Wannan shi ne zai sa ƙarancin kaya a kasuwanni da ƙara farashi kan ƙalilan ɗin da suka rage a hannun ‘yan kasuwa. Don haka tasirin abin zai shafi duk masu ruwa da tsaki a tsarin saye da sayarwa har da masu masana’antu zuwa ga tattalin arziƙi bakiɗaya.

Yana tsorata masu son zuba jari: Idan zanga-zanga ta yi zafi masu zuba jari za su fara jin tsoron zuba dukiyarsu, don kada a yi musu ɓarna. A saboda haka masu zuba jari na gida da na ƙasashen waje za su fara janye jiki da yin ɗari-ɗari kan don kada a lalata musu dukiya, a yanayin da babu kwanciyar hankali. Wannan zai sa harkokin kasuwanci da cinikayya su ja baya sosai.

Zai jawo ƙarin kashe kuɗi a wajen gwamnati: Saboda gwamnati da masu ruwa da tsaki za su yi ta ƙoƙarin ganin an shawo kan matsalar, wanda hakan ke sa kashe kuɗaɗen da ba a yi kasafi da su ba. Yana kuma ɗauke hankalin gwamnati daga gudanar da abubuwan cigaba da ta tsara, don ganin ta magance matsalar da ta kunno kai.

Daidaita haƙƙoƙi da tattalin arziƙi: Yana da matuƙar muhimmanci a duba kowanne ɓangare abin ya shafa dangane da ƴancin masu zanga-zanga da kuma samar da daidaito a fannin cigaban ƙasa ta fuskar tattalin arziƙi. A samar da fahimtar juna tsakanin ɓangaren gwamnati da masu shirya zanga-zanga, da kuma shugabannin al’umma, da jami’an gwamnati, don a fahimci koke-koken masu zanga-zanga da yadda za a duba yanayin da tattalin arziƙi ke ciki.

Kira na ga tattaunawa da samar da mafita

Ina kira ga duk waɗanda ke da ruwa da tsaki a wannan batu, su gayyato masu ƙoƙarin shirya wannan zanga zanga a zauna da su a tattauna yadda za a samu maslaha da yarjejeniya, don kada a samu ƙalubale a fannin tsaro da tattalin arziƙi. Na yi imanin Gwamnatin Tarayya a shirye take ta tabbatar da ganin ba a samu cikas a zamantakewar ƴan Nijeriya da bunƙasar tattalin arziƙi ba.

  • Domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar marubucin Ibrahim Abubakar Lajada, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, kan wannan adireshin na imel [email protected] ko lambar waya +1 3143331112
By ukarofi