Zanga-zanga: Gwamnati Tarayya ta ayyana gidajen yari a matsayin wuraren da ba a yarda a keta ba

Spread the love

A yayin da a ke shirin zanga-zangar gama gari domin matsin rayuwa, gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta yarda a keta alfarmar gidajen yari 256 da ke ƙasar ba.

Shugaban hukumar da ke kula da gidajen yarin Haliy Bababa ya fitar da sanarwa ranar Talata a Abuja.

Sanarwar da ta fita ta bakin mai magana da yawun shugaban hukumar ACC Abubakar Danlami Umar ta ce “A tunkarar shirin zanga-zangar da a ke yi ta ranar ɗaya ga watan Agusta 2024, mu na sanar da ƴan Nijeriya cewa gidajen yari wurare ne da ba a yarda a keta alfarmar su ba. Don haka muna gargaɗin mutane da su guji yi wa wuraren kutse.”

Shugaban ya godewa ‘yan Nijeriya bi sa haɗin kai da su ke bayarwa a ko da yaushe. Kuma ya umarci mutane da su kai rahoton duk wani abu da su ka gani ba su yarda dashi ba ta hanyar kiran waya ko saƙon imel.

By ukarofi