Rundunar ƴan sanda ta janye jami’an ta aƙalla 30 masu muƙamin sufeto da wasu sauran waɗanda ke tare da mutane na musamman.
A wata sanarwa da SP Anas Muhammad a hedikwatar ‘yan sandan da ke jihar Imo, ya bayyana cewa waɗanda aka janye, zasu koma wuraren sabon aikinsu ranar Alhamis ɗaya ga watan Agusta.
