Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Idan akwai wasu nau’in marubuta da za a ware a kiransu da ‘yan baiwa to, Maryam Muhammad Sani tana daga cikinsu, musamman a rukunin marubutan zamani na onlayin. Allah Ya yi mata wata baiwa ta musamman, wanda ya sa ta iya tserewa sa’o’inta a fagen rubutu har ta yi musu fintinkau, a fagen rubutun gajeren labari. Ban da kasancewarta marubuciyar littattafan zube, harwayau, Mum Amnash kamar yadda aka fi saninta, ta kasance fasihiya ce a fagen rubutun waƙoƙi, kuma malama mai koyar da ilimin harshen Hausa da Turanci. Ita ce ta zama gwarzuwa ta uku a gasar Hikayata ta BBC Hausa na shekarar 2022, kuma gwarzuwa a wasu gasanni daban-daban na marubuta, musamman a shekarar 2022 da ta kasance mata tauraruwar shekara a rayuwarta. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, ABBA ABUBAKAR YAKUBU, marubuciyar ta bayyana burinta na rubuta littattafan yara na tatsuniya da na wasan kwaikwayo. A yi karatu lafiya.
MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.
MUM AMNASH: Assalamu Alaikum. Sunana Maryam Muhammad Sani, amma a duniyar rubutu an fi sani na da Mum Amnash. Ni marubuciyar ƙagaggun labaran zube ce, sannan ina gwada rubutacciyar waƙa. Bayan rubutu ina harkar gashe-gashen kayan ƙwalam da maƙulashe, ina kuma sayar da kayayyaki daban-daban da suka haɗa da, kayayyakin kicin da sauran kayayyakin amfanin gida na mata a yanar gizo. Lokaci bayan lokaci kuma ina haɗa man shafawa, sabulun ruwa na wanke-wanke, turaren ruwa na ɗaki da sauransu.
Ina da aure, da yara uku, Shahid, Nana da Ammar (Amnash) a nan na samu sunan Mum Amnash.
Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taƙaice?
An haife ni a Unguwar Hausawa Sabon Titi da ke hanyar gidan Zoo a Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano ta Najeriya, a ranar 23 ga watan Nuwamba na shekarar 1995.
Na yi karatun Alƙur’ani a tsangayu guda biyu, Makarantar Malam Muntari (Allah Ya gafarta masa) da kuma Makarantar Malam Saina. Sannan na yi Islamiyyar Jawahirul Ahabab Hausawa, a nan na yi sauka a shekarar 2011. A ɓangaren boko, na yi firamare a Hausawa Model Primary School daga shekarar 2002 zuwa 2008. Sannan na shiga sakandiren ‘yammata ta G.G.S.S Hausawa a shekarar 2008 zuwa 2014. A shekarar da na gama sakandire aka kawar da ni, kuma a ita na yi saɓi-zarce na ɗora N.C.E a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi. Na gama N.C.E a 2017. Daga nan na tsagaita, ban ɗora karatu ba sai a shekarar 2021 na shiga Jami’ar Bayero Kano (B.U.K) inda nake nazari kan harkar malanta wato Education da kuma Hausa. A yanzu haka na kammala koyarwar gwaji a makarantar maza ta G.S.S Ado Gwaram, muna shirye-shiryen fara karatun zango na farko a aji huɗu, wanda daga shi zan kammala digirin farko da yardar Allah.
Wanne abu ne ya faru a rayuwarki lokacin tasowarki wanda ya taimaka wajen inganta tarbiyyarki da tunaninki?
Alhamdulillah! Dole na gode wa Allah, la’akari da yadda iyayena, malamaina, maƙwabta da kakannina suka yi tsayuwar tsayin daka wurin ganin sun ɗora ni a turbar da suke da yaƙinin za ta haifar mini ɗa mai ido ta kuma ɗora ni a hanya mai ɓullewa. Tun ban san kaina ba, Aunty Mairo, wata ‘yar maƙwabtanmu take tafiya da ni Islamiyyar Jawahirul Ahbab, ta ajiye ni a gefenta; da yake a lokacin ita take koyar da ‘yan aji ɗaya. Tun tana ajiye ni a gefe, har ta fara saka ni a layin ɗalibai, don haka a cikin neman ilimi na buɗi ido. Makarantar allo kuwa, daga baya mahaifina ya saka ni, tun yana raka ni, har na gane hanya nake tafiya ni kaɗai. Ba a saka ni a firamare ba, sai da na shekara bakwai, wannan ya ba ni damar kasancewa da mahaifiyata Aishatu Saleh Haske (Allah Ya gafarta mata Ya yi mata rahama, tare da dukkan magabata) sosai. Ta kuma taka muhimmiyar rawa wurin koyar da ni haɗe da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna; takan kuma yi mini horo a duk lokacin da na saɓa ƙa’ida don a samu fa’ida. Ina aji biyu na firamare na iya karatun Hausa da taimakon mahaifiyata. Haka mahaifina, yana iyakar bakin ƙoƙarinsa wurin samar mini da duk abinda zai inganta rayuwata da jikinsa da aljihunsa. Ina aji ɗaya a babbar sakandire, na koma hannun kakannina, su ma sun yi rawar gani musamman koyar da ni ilimin zamantakewa. Kusan zan iya cewa, hannaye da yawa ne suka haɗu don tabbatar da na samu ingantacciyar rayuwa.
Wanne abu ne ya sa ki ka fara sha’awar rubutun adabi?
Tun da na iya karatun Hausa na dasa ɗambar karatu babu ji babu gani. A duk farkon zangon karatu idan mahaifina ya saya mini littattafai, na Hausa nake fara karancewa, irin su: Tatsuniyoyi Da Wasanni, Ka Koyi Karatu, Magani Jari Ce da sauransu. Ba na tsayawa nan, har na ƙanwata duk sai na bi na karance. Daga nan na fara nacin karatu. Littattafan Adabin Kasuwar Kano kuwa, ba na karanta su sosai, na dai fi zama a ba ni labari da baka, ko kuma na saurara a gidajen rediyo. Kwatsam, watarana wata ƙawata Sumayya Surajo Abdurrahman ta rubuto wani labari a littafi, wannan rubutun nata shi ya yi mini ƙaimi ni ma na rubuto nawa, ɗaya ƙawar tamu Hauwa Shu’aibu ita ma ta rubuto. Kowa ya kan karanta nasa, ga sauran ƙawayenmu. Wani lokacin kuma mu yi masanya. Da ma tare muke sauraren wani shiri da ake karanta labaran zube a gidan rediyo. A lokacin mun yi sauka, don haka sai bayan sallar la’asar ake biya mana littattafan addini. Kafin malamai su shigo, mu kuma mun gama saurara. A taƙaice dai, karatu, sauraro da kuma maƙwabtar masu rubutu ne suka ja hankalina har na dasa ɗambar gwadawa.
Ko za ki iya tuna labarin farko da ki ka fara rubutawa?
Ba zan iya tuna labarin da na fara rubutawa ba a takarda, sai dai jigon zamantakewar karkara ne. Amma a yanar gizo labarin da na fara fitarwa shi ne wanda na fara rubutawa a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017 shi ma ban kai shi ƙarshe ba na saki, don muna N.C.E ne a lokacin, na yi masa taken ‘Labarina’.
Wane ne ya fara koya miki yadda za ki yi rubutu, ko nuna miki ƙa’idojin rubutu?
A ɗabi’ata a duk lokacin da na je gari na tarar da kowa na da jela to, nakan tsinki ta ganye na maƙala ni ma, matuƙar ba ta yi karo da addini ko al’adata ba. Kusan babu wanda ya ce min in yi rubutu, ganin ana yi ne ni ma na gwada. Sai dai shugabar ƙungiyarmu Ummukulsum Y. Imam da Amira Adam, sun taka muhimmiyar rawa wurin ƙarfafa min gwiwa. ƙa’idojin rubutu kuwa, na ɗan san kaɗan da yake turancin English da Hausa na yi a N.C.E. Duk da haka Amira Adam ta taimaka matuƙa gaya wurin tunasar da ni wasu ƙa’idojin, a haka muka cigaba da gurgurawa. Likkafarmu ba ta ɗaga ba, sai da muka tsinci kanmu a wani zauren WhatsApp mai taken Majalisar Marubuta. Duk da babu wanda na sani a zauren sai Amira, hakan bai sa mun yi biris da duk wani gyara da za a yi wa wani ko wata ba. Haka ban yi ƙasa a gwiwa ba, ina bibiyar shirye-shiryen da ake yi a wannan zauren musamman Ranar Sharhi, wanda Nana Aicha Hamissou Abduolaye take gabatarwa. Ni ma na tura labaraina an yaba an kuma fitar mini da kurakuraina. A sanadin hakan Nana Aicha ta fara taimaka min da gyara a rubutuna. Sannan akwai Jannat M. Nasir, ita ma ta taka muhimmiyar rawa wurin nusar da ni.
Sannan na shiga group ɗin Marubuta na Malam Bamai Dabuwa, da kuma Aji Na Muhamman na Malam Jibrin Adamu Rano. A waɗannan zauruka na ƙara sanin ƙa’idojin rubutu, da dabarun gina labari musamman gajeren labari.
Wacce shekara ki ka fara fitar da rubutunki kuma kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?
A shekarar 2016 zuwa 2017, amma cikakken labari a 2018 na fara yi. Kuma duka labaraina a yanar gizo suke, ban taɓa wallafawa ba; sai guda ɗaya da muka yi haɗaka wurin rubuta shi. Na rubuta labarai guda takwas:
‘Labarina’, ‘Yammatana’, ‘Ladiyo ‘Yar Bana’, Dafta A’ihya, Tarkussalat, So Ko Wahala, ‘Yar Hisba’, ‘Rai Da Motsi’, ‘ɗaya A Cikin Dubu’ (Haɗaka), sai kuma gajerun labarai waɗanda za su iya kai wa 20 -zuwa 30.
Me ya sa ki ka fi mayar da hankali kan rubutun gajerun labarai a maimakon cikakken littafi?
Kusan ba na cikin mutanen da ke iya haɗa taura biyu ko uku a baki na kuma tauna a lokaci guda. Ko da na haɗa, nakan raja’ar da hankalina ga ɓangare guda. Duk yadda naso haɗa rubutu da makaranta, karatun na rinjaya ta, sannan ga ƙarancin lokaci. Kusan duk dogayen labaran da na rubuta har ƙarshe, na rubuta su ne bayan na kammala N.C.E kafin na ɗora karatu. ‘Rai Da Motsi’ ne kaɗai na yi, shi ma kuma labarin gasa ne. Sai kuma ‘Ɗaya A Cikin Dubu’, wanda haɗaka muka yi wurin rubuta shi tare da gwarazan Hikayata 2022. Dalili na biyu kuwa da ya sa na jingine rubutu bayan makaranta, bai wuce hanƙoron son ganin na koyi rubuta gajeren labari ba. Wannan ya sa na yi ta gwadawa, har na ɗan fara gane makamarsa.
Waɗanne labarai ne ki ka rubuta waɗanda suka fi shahara, ko jawo miki da wata nasara? Kawo mana sunayensu da bitar 3 a ciki.
Daga cikin labaraina da suka shahara da kuma cimma nasara akwai: ‘Dafta A’i’hya’, ‘Mugun Gani’, ‘Al’ummata’, ‘Takwara’, ‘Rai Da Motsi’ da kuma ‘ɗaya A Cikin Dubu’ (Haɗaka).
Shi littafin ‘Dafta A’i’hya’ labari ne da ko da sunansa za a gane naƙasuna dangane da sanin ƙa’idojin rubutu a lokacin. Wannan labarin ya jawo mini nasarar samun mabiya matuƙa gaya. Hasali ma, ina tsaka da rubuta shi, Allah Ya karɓi ran mahaifiyata, sai da na share watanni shida sannan na dawo yanar gizo. Amma ko da na ɗora, kai tsaye masu bibiyar shi suka tunasar da ni ainihin inda na tsaya. Ni kuma na so taƙaita shi ne, don na kammala a fejika kaɗan, haka na cigaba da ja har na kammala shi.
‘Dafta A’i’hya’, labari ne da yake ɗauke da jigo hatsin bara, da farko na fara labarin da barkwanci sosai, don a lokacin na barkwancin sun fi karɓuwa ga makaranta. Tauraruwar labarin Aisha, ma’aikaciyar jinya ce, ina ya Allah, babu ya Allah! Ta faɗa soyayya da wani Bayarabe, wannan ya ɗaga hankalin mahaifinta. Ya kuma nisanta ta da jihar da take zuwa ƙauyen Taka-Tsaba, wanda ƙanin abokin mahaifinta shi ne dagacin garin, don ta taimaka musu kasancewar babu likita ko ma’aikata a asibitin garin. Da wannan damar ya yi amfani, wajen jifan tsuntsu biyu da dutse guda. A ƙarshe bayan an turza ta auri Tajuddin duk da bambancin ƙabilar da ke tsakaninsu. Daga baya kuma mai rabawa don dole ta raba su, sai ta auri wani likita Khubaib wanda ɗa ne ga Dagacin Taka-Tsaba. Daɗin daɗawa a cikinsa akwai abinda ya shafi kishi tsakanin kishiyoyi, kissa da kisisina da ma yadda kishiyar da ta zama ‘yar’uwa take taka muhimmiyar rawa wurin inganta rayuwar abokiyar zamanta.
Sai kuma littafin ‘Al’ummata’, wanda labari ne gajere da ya zo mataki na uku a gasar Hikayata ta BBC Hausa; wanda ban taɓa zato ko tsammanin zan samu nasara a kansa ba, sai dai cikin ƙudirar Allah Ya kai wannan matakin. Haƙiƙa na samu nasarori da dama, sanadiyyar wannan labarin.
Akwai kuma ‘Tauraruwar Hauwa Kulu’, wacce mazauniyar karkara ce da Allah Ya tarfa wa garinta nono ta samu nasarar shiga makarantar gaba da sakandire, duk da ta kasancewar ta marainiya. Goyon kaka sai ya yi mata amfani wurin cimma burinta, wanda a ƙauyen ba a taɓa samun macen da ta taɓa kai wa wannan matakin ba. Nan da nan ta fara ƙamshin Turare ɗan goma, la’akari da ƙaunar da ‘yan garin ke nuna mata, ganin yadda take amfanar da su kan duk wani abu da ake buƙatar rubutu, buɗe asusun banki da sauransu. Saɓanin sauran yara mazan da kan yi ƙaura zuwa birni su nemi aiki su zauna a can, ba tare da sun yi tunanin waiwayar sun bar baya da ƙura ba.
Zaman Hauwa Kulu a birni yayin karatu, ya sa ta samu wayewa da gane zambar da ‘yan siyasa ke yi musu, don haka ta fara zuwa kafafen watsa labarai ta saka shuwagannin ƙaramar hukumarsu a gaba. Daga baya kuma ta fara amfani da yanar gizo wurin haɗa hotunan makarantun ƙauyensu, asibitoci, hanyoyi, da kuma waɗanda ‘ya’yan ‘yan siyasarsu ke yi. Wannan ya ɗaga hankalinsu suka koma barci da ido ɗaya. Duk yadda suka so gano ta, abin sai ya ci tura, don tana ɓatar da sawu, tana kuma yi wa kanta laƙabi da Majadin Maijaki, sannan tana turbuɗe fuskarta da hoda da gazal, wannan ya sa ko an ɗauki hotonta ba ya bayyanar da ainihin fuskarta. A ƙarshe dai asirinta ya tonu bayan ta ɗebo da zafi. Ba tare da tunanin abin da zai je ya dawo ba, ta taɓa gwamnan jihar, aka zo har ƙauyen aka yi mata bugun sakwara, tare da yaɗa ƙirƙirarrun hotunan ɓatanci da aka dasa fuskarta. Duk da mutanen garin na ganin za ta aika, tun da ta ƙi aure, amma daga baya da aka kai ta kotu a birni, sai suka bi ta, suka kuma goya mata baya domin sun gane tana kishinsu matuƙa. Kafin a kori shari’ar ta dawo, matasan ƙauyen sun saya mata form ɗin takara kuma ba ta ƙi ta tasu ba ta rattaɓa hannu. Ana ji ana gani, mace da ake ganin ba za ta iya ba, ta samu nasarar zama shugabar ƙaramar hukumarsu.
Shi kuma littafin ‘Rai Da Motsi’, labari ne da na shiga da shi gasar Gusau Institute a shekarar 2022. Sai dai bai tsallaka matakin ƙarshe ba. Iyakacinsa na farko.
Babbar nasarar da na samu a sanadin ‘Rai Da Motsi’, ba ta wuce yadda manyan marubuta da manazarta suka ƙarfafa mini gwiwa ba, tare da yaba ƙoƙarin da na yi a wannan labari. Wannan Ya daɗa yi mini ƙaimi wurin ɗaura aniyar ƙara rubuta wasu dogayen labaran. Har zuwa yanzu, ina kan ƙara gyara labarin ‘Rai Da Motsi’, kafin na buga shi.
Labari ne da aka gina shi a kan nakasa, wadda ba ta taɓa zama kasawa matuƙar da rai kuma an motsa. Mas’uda (Uda) ita ce tauraruwar labarin, ta kuma nakasa sanadin rashin ƙwarewar wasu ma’aikatan asibitoci masu zaman kansu. Ta rasa hannunta guda ɗaya. Duk da haka mahaifiyarta ta yi tsayuwar tsayin daka wurin ba ta ilimi, don ta samu rayuwa ingantacciya. Sai dai ba cinya ba ƙafar baya, ta haɗu da ƙalubale daban-daban har ta kai ga ta kusa sarewa. Tana samun masu son aurenta, amma mahaifansu da ‘yan’uwa kan yi tsallen baɗake su ƙi amincewa saboda nakasarta. Saurayinta na ƙarshe kuwa, sai ana tsaka da shagalin biki maganar ta lalace, wannan tashin hankalin ya sa ta nufi ƙauyensu duk da kakar mahaifiyar tata tana can inda ta baro. A yayin wannan tafiya ce, ta yi karo da abin da ya tunatar da ita, har ta gode wa Allah, tare da jin ƙwarin gwiwar tunkarar rayuwa a duk yadda ta zo. Wata yarinya ta gani a mota, a take ta tuno da lalurar nakasar ƙwaƙwalwa wato ‘Down Syndrome’, wadda wani likita ya taɓa yi mata bayani a kanta. Wannan lalurar tana afkuwa ne, sakamakon daɗuwar ƙwayar halitta; sakamakon haka kuma a samu naƙasu a bunƙasa da ginuwar jiki har da ƙwaƙwalwa. Da yake mai ido ɗaya ba ya gode wa Allah sai ya ga makaho, wannan ya sa ta tsaya tsayin daka ta taimaka wa jaririyar. Ita ma kuma a ƙarshe, ta yi katarin samun abokin burmin da ya yi daidai da ƙwaryarta.
Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako ƙungiyar ke miki a rubuce-rubucenki?
Ina cikin ƙungiyoyi guda biyu. Haɗaka Writers’ Association, da kuma Gamayyar Marubutan Jihar Kano (GAMJIK). Babu shakka ƙungiyar Haɗaka ta taimaka min matuƙa gaya, wurin watsa labaraina a yanar gizo da kuma zaurukanta. ƙungiya ce da ta yi tsayuwar tsayin daka wurin tsefe rubutun ‘ya’yanta gudun kar a yi kitso da ƙwarƙwata. Ina matuƙar jin daɗin ƙungiyar saboda yadda ta barranta ga rubutu duk abin da ya yi karo da tarbiyyar addini da kuma al’ada.
Ita ma kuma Gamayyar Marubutan Jihar Kano (GAMJIK) wacce ta kasance uwa ce ga sauran ƙananan ƙungiyoyin marubuta ‘yan Jihar Kano da ma mazauna Kano. ƙungiyar tana yin duk mai yiwuwa wurin ganin ta kawo cigaba ga marubuta. Hasali ko a satin nan, ƙungiyar ta yi nasarar gabatar mana da marubuci Malam ɗanladi Z. Haruna don ya koyar da mu yadda ake amfani da Gmail da kuma Blog, ganin yadda marubuta da dama kan samu matsala a yayin tura saƙo ko labaran gasa; idan aka yi rashin katari sai su rasa wannan dama. Haƙiƙa ina amfanuwa da GAMJIK sosai.
Waye a cikin marubuta ya zama miki madubin kwaikwayo a salon rubutunsa ko gogewarsa?
A marubutan dauri, Marigayi Alhaji Abubakar Imam shi ne allon kwaikwayona. Allah Ya gafarta masa, Ya yi masa rahama. Ba ni da buri a harkar rubuce-rubuce da ya wuce a ce na samar da littattafan da yara ‘yan firamare da sakandare za su dinga amfani da su a darasin Hausa don na cusa musu kishin harshe, kishin ƙasa da kuma sanin kai.
A marubatan littattafan Adabin Kasuwar Kano kuwa, ina son rubutun Aunty Jamila Umar Tanko (JUT) da Aunty Fauziyya D. Sulaiman. Idan kuwa aka dawo gida, wato cikin marubutan yanar gizo to, na iya cewa duk marubucin da yake rubutu mai ma’ana da zai amfanar da al’umma matuƙar bai sauka daga turbar addini da al’ada ba allon kwaikwayo ne a gare ni. Hasali suna da yawan da ba zan iya lissafo su ba. A cikinsu akwai malamaina, ƙawayena, yayyena, sa’annina da kuma ƙannena a fagen rubutu. Duk ina amfana daga gare su.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
