Zanga-zanga: Mataimakin Gwamnan Neja ya yi wa NLC mubaya’a

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Comrade Yakubu Garba, ya yi wa Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar mubaya’a game da zanga-zangar lumanar da ta fara gudanarwa a wannan Laraba.

Da yake jawabi a wajen taron, Garba ya bai wa ƙungiyar muhimman shawarwari da kuma hanyoyi da ya kamata ta bi wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta don amfanin al’umma baki ɗaya.

Manhaja ta kalato cewar, Mataimakin Gwamnan shi ne shugaban ƙungiyar ƙwadago a jihar gabanin tsayar da shi takara a matsayin mataimakin gwamna.

Majiyarmu ta ce jami’an da suka mara masa baya ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Hon Abdulmalik Sarkin Daji.

NLC ta fara gudanar da zangaine domin neman cim ma buƙatunta a wajen gwamnati da suka haɗa da samar da ingantattun hanyoyin da za su rage wa ‘yan ƙasa raɗaɗin cire tallafin mai.