Zanga-zanga: ‘Yan sanda sun kama lauyan Nnamdi Kanu da wasu a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an ƴan sanda sun cika hannu da Aloy Ejimkor, wanda shi ne lauyan da ke kare tsararren jagoran Ƙungiyar masu fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), wato Nnamdi Kanu a yayin da ake zanga-zanga a Abuja.

Lauyan ne ya bayyana kamen ta shafinsa na kafar X a yau Litinin, 20 ga watan Oktoba, 2025.

Ejimakor ya bayyana cewa an kama shi ne da wasu da dama a lokacin da ake gangamin kiran a sako Nnamdi Kanu a Birnin Tarayyar.

Da fari lauyan ya zargi ƴan sanda da fesa wa dandazon ƴan zanga-zangar hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa su.

A yau ne masu jama’a suka yi tattaki acikin garin Abuja da nufin gangamin neman sako Kanu, wato ‘#FreeNnamdiKanuNow’, wanda hukumar ƴan sandan farin kaya DSS, ta tsare tun a watan Yunin 2021.

By Babaji