Zargin ɓata suna: Ɗan jarida ya maka jaridar Daily Trust, Gwamnatin Nasarawa da Yakubu Lamai a kotu

Daga WAKILINMU

Tsohon ma’aikacin jaridar Daily Trust ya maka Daraktan Yaɗa Labarai ga Gwamnan Jihar Nasarawa, Mr. Yakubu Lamai, da jaridar Daily Trust da kuma Gwamnatin Jihar Nasarawa a gaban kuliya bisa zargin ɓata masa suna.

Ibraheem Hamza Muhammad wanda tsohon wakilin jaridar Daily Trust ne a jihar Nasarawa, ya maka waɗanda yake zargin da ɓata masa suna a kotu ne ta hannun lauyansa, Barrister M. A. Danmama.

Yayin zaman farko na sauraron shari’ar a Babbar Kotun Jihar Nasarawa mai zamanta a New Karu a ranar Talata, mai ƙarar ya yi iƙirarin cewa ya haɗa wani labari bayan kammala bincikensa yadda ya kamata wanda aka wallafa a shafin intanet na jaridar Daily Trust mai taken: “Babu na’urar taimakon numfashi ko guda amma Gwamnatin Nasarawa ta saya wa ‘yan majalisa motocin miliyan N500.”

Ga adireshin cikaken wannan labarin kamar haka: https://dailytrust.com/amp/no-single-ventilator-but-nasarawa-buys-n500m-cars-for-lawmakers.

Kodayake, daga bisani Daraktan Yaɗa Labarai ga ga Gwamnan Jihar Nasarawa, Mr. Yakubu Lamai ya maida martani kan labarin kamar yadda za a iya gani a wannan adireshin na ƙasa: https://dailytrust.com/rejoinder-no-single-ventilator-but-Nasarawa-buys-N500m-cars-for-lawmakers

Ibraheem Hamza Muhammad, ya roƙi kotun da ta sanya a biya shi kuɗi har Naira miliyan ɗari uku (N300,000,000:00) saboda ɓata masa suna da ya ce an yi.

A nasu ɓangaren, lauyoyi masu kare waɗanda ake zargin, Barrister Felix Dza da E.J Ittah da F.C. Uzowuru dukkansu sun buƙaci kotun da ta ba su lokaci don su koma su shirya bayanan kare waɗanda suke bai wa kariya a gaban kotun.

Kotu dai ta amince da buƙatar lauyoyin inda alƙalin kotun, Justice Hannatu Kabir ta ɗage shari’ar ya zuwa ranar 27 ga Janairun 2022.