
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za su gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar don yi masu hukunci bisa zargin cin zarafi.
Mataimakin Mai Tsawatarwa na majalisar, Onyekachi Nwebonyi a wata hira da gidan talabijin na ‘channels’, ya ce waɗanda lamarin ya shafa za su yi wa kwamitin bayani game da abinda suka sani akan zargin cin zarafin, wanda Natasha ta ɗora wa Akpabio.
Ya ce, za su yi hakan ne don bai wa kowane ɓangare damar gabatar da hujjojinsa.
Natasha, wadda ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne ta yi ikirarin cewa lamarin ya faru ne a Disambar 2023 a lokacin da ita da mijinta suka kai wa Akpabio ziyara a gidansa dake Uyo, Babban Birnin Jihar Akwa-Ibom.
Ta ce, a yayin ziyarar tasu ne Akpabio ya riƙe hannunta da nufin yin zagaye acikin gidan, inda daga baya ya nemi yi mata rashi ɗa’a duk da cewa mijinta yana nan.
Amma, mataimakin Mai tsawatarwar ya zarge ta da ƙoƙarin karkatar da hankulansu kasancewar ba ta bada gamsassun hujjoji ba game da zargin.
Ya ce, ya na ɗaya daga cikin sanatocin da suka halarci gidan a ranar da ta ce abin ya faru, don haka za su faɗi abinda suka gani a yayin zaman hukuncin.
Kwanaki kaɗan bayan haka ne aka dakatar da ita a majalisar bisa laifin saɓa wa dokokin majalisar bayan ta gabatar da ƙorafi akan zargin cin zarafin da wasu batutuwa.
Daga bisani ta garzaya majalisar dokoki ta mata a ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta shigar da batun don neman a yi mata adalci.
