Zargin garkuwa da fyaɗe: Sarkin Daura ya sauke dagacin Mantau

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq, ya tuɓe Iliya Mantau daga sarautar dagacin Mantau na garin ‘Yarmaulu, dake ƙaramar hukumar Ɓaure ta Jihar Katsina.

Masarautar ta Daura ta sauke basaraken sakamakon zarge-zargen hannu da ake ma sa na garkuwa da wata mata tare da yi mata fyaɗe.

An sanar da dakatarwar ne, bayan samun koke-koke daga al’ummar garin wanda ya kai ga zanga-zangar matasa a makon da ya gabata.

Matasan sun bayyana damuwarsu kan yadda ake zargin dagacin da hannu kai tsaye cikin lamarin da ya haɗa da sace matar aure mai suna Zulaihatu tare da ɗan jaririnta, da kuma yi mata fyaɗe bayan karɓar kuɗin fansa.

Sarkin Daura, a lokacin da yake sanar da tsige dagacin, ya jaddada cewa masarautar Daura ba zata lamunci duk wani abu da zai tauye rayuwar talaka, yana mai bayyana cewa ƙofar masarautar a buɗe take ga kowane ɗan kasa da ke da ƙorafi ko koken zalunci.

“Idan wani ya ji an cuce shi, ko da ɗan da na haifa ne, ya zo ya gabatar da ƙorafinsa a masarauta. Wannan masarauta ce ta talakawa,” in ji mai martaba Sarkin.

Ya ƙara da cewa: “Wannan masarauta ta taɓa tuɓe wanda ta naɗa, kuma Sarki Abdurrahman ya taɓa daure ɗansa a bisa laifi. Shi ya sa ba za mu lamunci cin zarafin kowa ba.”

Daga ƙarshe sarkin ya buƙaci al’umma da su ci gaba da yin biyayya tare da bin doka da oda gami da miƙa koke kokensu ta hanyoyin da suka dace domin a bi masu haƙƙin su.

By ukarofi